Monday, 13 March 2017

BUGYATUL MISHTAQ

BUGYATUL MISHTAQ❗
Kamar kowace Lahadi yauma mun dora inda muka kwana acikin wannan littafi na BUGYATUL MISHTAQ.
IBN TAIMIYYAH yake cewa haqiqa ALLAH (S.W.A), Yana hadama bawa nau'i na ni'ima wanda ya wajaba ya gode masa, ko kuma jarabawa wadda ya wajaba yayi haquri akanta, kamar yanda abun ya kasance ranar 27 ga watan Ramadhan ranarne akayi yaqin BADAR, Kuma irin ranarce aka kashe SAYYIDINA ALIYU, Hakanan kuma abunda yafi shahara cewa ranar litinin acikin watan RABI'U AUWAL ne aka haifi MANZON ALLAH (S.A.W), Kuma a irin lokacinne yayi HIJIRA, kuma a irin ranarne ya rasu. Don haka kenan bawa mumini za'a iya jarabtarsa da abubuwa masu kyau wadanda zasu faranta masa rai, da kuma musibobi wadanda zasu baqanta masa rai duk alokaci guda, domin Dan Adam ya kasance mai haquri kuma mai godiya, to ya kake ganin abun idanya kasance a lokutta biyu  lissafafi daga nau'i guda.
Aqarshe IBN TAIMIYYAH Yayi bayanin dalilin rubuta wannan littafi cewa wasu jama'ane suka isko IBN TAIMIYYAH  da wata takarda wadda 'yan shi'ar Iran suka rubuta masu, sai IBN TAIMIYYAH ya karanta wannan takardar aqarshe ya walwale masu matsalar kuma suka gamsu suka fahimta.
Wannan kadan kenan daga cikin abunda karatun yau ya qunsa, don jin cikakken karatun a tarbi audio da zamu turo bada dadewaba insha Allah.
Muna roqon Allah ya sakawa mal da alkhairi amin thumma amin.

No comments:

Post a Comment