Monday, 26 June 2017

2017 RAMADAN TAFSEER

*2017 COMPLETE  RAMADAN  TAFSEER*

   COMPLETE  2017 RAMADAN  TAFSEER DAGA MASALLACIN JUMA'AH NA ABU HURAIRA AREA  II TSAFE.

  wanda Malam Sani Liman Tsafe (ABI HURAIRA)   yake gabatarwa a Area II Tsafe, jahar Zamfara  Nigeria.

Shiga  links dake kasa  Domin saukewa Cikin sauki ka saurara  Cikin kyakykyawan Sauti.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

01 Ramadan Tafseer 1438Ah Suratul Nisa i By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24378

02 Ramadan Tafseer 1438 Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24379

03 Ramadan Tafseer Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe
http://darulfikr.com/s/24380

04 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24381

05 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Sani LimanTsafe
http://darulfikr.com/s/24382

08 Ramadan Tafseer Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24383

09 Ramadan Tafseer Akan Hukunce Hukunce Mata Na Dare By Mal San Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24384

10 Ramadan Tafseer Na Dare By Abu-Hurairah Tsafe
http://darulfikr.com/s/24385

11 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24386

12 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24387

14 Ramadan Tafseer 1438 Suratul Ma ida By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24388

15 Ramadan Tafseer Na Dare Suratul Ma ida By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24389

16 Ramadan Tafseer 1438 Na Dare By Mal SaniLiman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24390

17 Ramadan Tafseer Na Dare 1438 By Mal Sani Liman Tsafe
http://darulfikr.com/s/24391

19 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24392

20 Ramadan Tafseer 1438 Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24393

21 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24394

Kasance do darulfikr.com a koda yaushe domin  samun karatuttukan maluman  sunnah.

*_Hashim Surajo Uba Tsamiya (ABU SINAAN)_*

http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com

2017 RAMADAN TAFSEER

*2017 COMPLETE  RAMADAN  TAFSEER*

   COMPLETE  2017 RAMADAN  TAFSEER DAGA MASALLACIN JUMA'AH NA ABU HURAIRA AREA  II TSAFE.

  wanda Malam Sani Liman Tsafe (ABI HURAIRA)   yake gabatarwa a Area II Tsafe, haha Zamfara  Nigeria.

Shiga  links dake kasa  Domin saukewa Cikin saki LA saurara  Cikin kyakykyawan Saudi.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

01 Ramadan Tafseer 1438Ah Suratul Nisa i By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24378

02 Ramadan Tafseer 1438 Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24379

03 Ramadan Tafseer Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe
http://darulfikr.com/s/24380

04 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24381

05 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Sani LimanTsafe
http://darulfikr.com/s/24382

08 Ramadan Tafseer Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24383

09 Ramadan Tafseer Akan Hukunce Hukunce Mata Na Dare By Mal San Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24384

10 Ramadan Tafseer Na Dare By Abu-Hurairah Tsafe
http://darulfikr.com/s/24385

11 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24386

12 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24387

14 Ramadan Tafseer 1438 Suratul Ma ida By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24388

15 Ramadan Tafseer Na Dare Suratul Ma ida By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24389

16 Ramadan Tafseer 1438 Na Dare By Mal SaniLiman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24390

17 Ramadan Tafseer Na Dare 1438 By Mal Sani Liman Tsafe
http://darulfikr.com/s/24391

19 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24392

20 Ramadan Tafseer 1438 Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24393

21 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24394

Kasance do darulfikr.com a koda yaushe domin  samun karatuttukan maluman  sunnah.

*_Hashim Surajo Uba Tsamiya (ABU SINAAN)_*

http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com

IN ANSHA RUWA...

IN ANSHA RUWA A KOMA AIKI

*IN ANSHA RUWA A KOMA AIKI!!!*

Karatun littafin NIHA YATIL ÃLAM wallafar Dr.Muhammad Abdulrahman Al-arify, karatun da *USTAZ MUSA S LAWAL TSAFE* ya fara gabatar mana a jiya SALLAH 01/10/1438AH
25/06/2017AC
Malam ya fara mana da mukaddimar littafin, kuma littafin yana magana akan alamomin tashin kiyama Manya da kanana.

Daure ka sauke wannan karatun yana da amfani matuka
👇👇👇👇👇👇👇👇
نهاية العالم د. العرفي
DAGA BAKIN; *USTAZ MUSA S LAWAL TSAFE(ABU SALIH IBN SALIH)*

http://darulfikr.com/s/24541

darulfikr.com takuce domin yada sunnah.

Copyright©
*_Hashim Sirajo Uba Tsamiya (ABU SINAN)_*

+2348064734911
+2349030201868

Saturday, 3 June 2017

HUDUBAR JUMU'AH

HUDUBAR JUMU'A
A  MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin  Massallaci Jumu'a Na Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na Liman'

Yayi Hudubar Sane Akan #TSAFTA

Godiya ta tabbata madaukakin sarki, Muna gode masa muna neman taimakonsa, Muna neman yakare daga sharrin kawunan mu,

Na shaida babu abun bautawa da gaskiya sai ALLAH Baya da abokin taraiya, Na shaida Annabi Muhammadu bawan sa ne kuma manzonsa,

Tsira da amincin ALLAH Su kara tabbata ga manzo tsira da alayen da sahabban sa da dukan wadanda suka bayan su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako!

Yan uwa musulmi a yau khudbar zatayi magana ne akan Tsafta a addinin musulunci!

Addinin musulunci yayi umarni da tsafta a kowane bangare na rayuwa, Kama daga ta jiki da kaya da dukan dai wata mu'amula ta yau da kullun,

Tsafta tana daya daga cikin umarni na farko farko da aka fara bayarwa a lokacin da musulunci yake da dumi duminsa,

Kamar yadda ALLAH Yake fada cikin suratul Muddasir cewa ''YA KAI MAI LULLUBI (Annabi Muhammad SAW) KA TASHI KAYI GARGADI KA GIRMAMA UBANGIJINKA KA TSAFTACE TUFAFIN KA''

Kunga wannan ayar tana kwadaitar damu kan tsafta, Hakama ALLAH Madaukakin sarki na cewa ''YAKU WADANDA KUKAYI IMANI IDAN KUN TSAYU GA SALLAH KU WANKE FUSKOKINKU DA KAFAFUNKU''

Yaku yan uwa musulmi kusani itafa tsafta ita ke jagoranta har mutane su soka su dinga taraiya dakai,

Yaku yan uwa musulmi daga cikin manyan ni'imomin da ALLAH Yayi mana itace ni'imar ruwan sama, Su kuwa ruwan sama suna zuwa ne dan tsaftace kasa daga datti, Da kazanta da shirka wadda shaida L.A ya qawata ma mutane yi, Kamar yadda ALLAH Madaukakin sarki yake cewa ''MUNA SAUKAR DA RUWAN SAMA DAN TSAFTACE KASA DAGA DATTI''

Yaku yan uwa musulmi tsafta tana da wani bagire a musulunci, Manzo rahama SAW Yana fada cikin wani hadisi cewa ''MAI TSAFTA ALLAH ZAI TADASHI YANA HASKE A FUSKA'' Ma'ana mai alwalla ita kuwa alwallah tsafta ce,  Hakama manzo rahama SAW Yana fada cewa ''RANAR KIYAMA AL'UMMATA ZASU ZO DA HASKE A FUSKOKIN SU DA KAFAFUN SU SABODA ALWALLAR DA SUKA AIKATA A DUNIYA''

Tsafta muhimmacinta nada matuqar yawa, shinasa sa aka alaqanta duk wata ibada da tsafta kamar su sallah, Dawafi Karatun Qur'ani da sauran ibadu,

Yana daga cikin tsafta yawaita wanka kamar su na jumu'a kamar yadda manzon rahama SAW Yake cewa ''NAYI UMARNI DA WANKAN JUMU'A''

Hakama a wata ruwayar na cewa ''WANKA JUMU'A WAJIBI NE''

Mafi yawan wasu mutane na ganin kamar tsafta batada wata alaqa da addinin musulunci, Sam ba haka bane addinin musulunci shine addinin daya fara jaddadda tsafta a duniya,

Rashin tsafta dabi'ar ce ta mushrikai, Wata rana salmanul farisi ya fito sai wani mushriki yayi mai wata magana ta izgili yana cewa ''Naga abokin (wato yana nufin annabin Muhammad SAW) ku yana umartar ku da tsafta har a makeyi''

Hakika musulunci ya sanya tsafta a ciki yanki na imani, Kamar yadda hadisin manzon Tsira yake cewa ''TSARKI SHARADI NE NA IMANI'' Kaga idan kana da kazanta to lallai imanin ka nada rauni matuka!

Saboda matsayin tsarki da tsafta yasa malaman fiqhu suke yawaita gabata da tsafta ko tsarki a farko farko,

ALLAH Madaukakin sarki ya yabi mata kan yadda suke tsafta kamar yadda yake fada a cikin suratul baqarah cewa ''LALLAI ALLAH YANA SON MASU TUBA DA MASU TSAFTA''
Ana bukatar duk bayan mata sunyi tsarki na kowane jini suyi tsarki dan tsafta su sanya turare,

Musulunci yana wajabta wasu fannona da suka zama wajibi a aikata su har guda goma sha daya (11)

1- Tsaftace baki, Ma'ana tsaftace baki ta hanyar wankewa da Brush da macling, Ko aswaki ko wani mai na goge baki, kamar yadda hadisi ya umarta cewa ''KUYI ASWAKI DAN YANA TSAFTACE BAKI DAGA KAZANTA''

2-Tsaftace suma ko gashin kai, Ma'ana tsaftace gashin kai, Ko rage sa, Ko kuma shace sa, Ko kuma askesa, Hadisi daga manzo tsira na cewa ''WANDA ALLAH YA AZURTA DA GASHI YARINGA KARRAMA GASHIN'' Ma'ana ka tsaftace shi ta dawanchan hanyoyi, Kada kabar gashin ka lalace yayi babu kyan gani ba tsafta.

3-Tsaftace gidaje da massalatai da kofar gidaje da wurare kasuwanci, Kada kubar wajen shara ta taru ko kuma yayi kasha-kasha, hadisi ya tabbata daga manzo tsira cewa ''KU TSAFTACE FARFAJIYAR KU KADA KUYI KOYI DA YAHUDAWA DAN SUNA TARA SHARA TSAKAR GIDA ''

4-SANYA TURARE Ma'ana yawan amfani da turare dan kauda wari da kazanta, Anan ma hadisi ya tabbata daga manzo tsira cewa ''LALLAI ALLAH MAI KYAU NE KUMA YANASO YAGA ANA TSAFTA''

5-Tsaftace Massallatai, Kada mubar massallatan mu babu kyau, Annabi ya gargademu da kada muje massallaci ba tsafta ''WANDA YACI ALBASA KO TAFARNUWA KADA YAZO MASSALLACI''

6- Mata masu jinin al'ada ya zama wajibi su kyautata tsafta, yana da kyau su warware kitson su, su wanke ko ina tare amfani da turare a gabansu dan inganta tsaftar su,

7-Tsaftace jiki, Mu kula da tsaftace jiki ganin yadda yanzu muke cikin lokachin zafi, Kamar yadda yagabata khudbar wancan makon

8-Kula da sunnoni goma, Manzo tsira SAW Yana cewa ''YANA CIKIN FIDDA WATO (Sunnar asali ta yan adam) sune kamar haka,
-Rage gashin baki, a kula ba askewa ake nufi ba baki daya,
-Mucika gemu, Kammala gemu ba tare aske shi ba,
-Aswaki, Yawaita aswaki yana daga cikin sunnonin asali,
-Kuskure baki, Yawaita kuskure baki idan kaji yadan yi maka nauyi,
-Rage akaifa, A yawaita rage akaifa saboda akaifa shine ne ke daukar datti ta boye a cikin hannu
-Wanke hannu, Yawaita wanke hannu, Dan gudun kada a kwaso wata cuta,
-Rage gashin hamata, Yana da kyau rage ya, Dan anan cuttutuka suke boyewa,
-Gusar da gashin mara, Hadisi yazo daga manzo tsira cewa ''KADA MUSULMI YA KUSKURA YA WUCE KWANA ARBA'IN BAI KAUDA WADANNAN KAZANTAR BA''

9-Tsaftace hanyoyin da muke bi, Mu tsaftace hanyoyin da muke bi yau da kullun, Hadisi yazo daga manzo tsira cewa ''IMANI GIDA SABA'IN NE BABBA DAGA CIKI ITACE KALMAR LA'ILAHA ILALLAH KARAMA DAGA CIKIN KUWA ITACE GUSAR DA DATTI HANYA''
Yana da kyau koda gwalab ko fitila ce a aje a hanya dan ganin haske a hanya

10-Tsaftace abinci da ruwan mu, Kiyaye ruwan sha dana koramu, Da kuma tsaftace abinci, Manzo tsira SAW Yace ''IDAN KUN SHIGA GIDA KU KULLE IDAN ZASU KWANTA KU RUFE RANDA KU KASHE WUTA KU RUFE ABINCI'' saboda shaidan baya iya buda randar da aka rufe ko abincin da aka rufe, Yana da kyau a kula, Idan ba'a rufewa shaidan zai iya zuwa ya tofa miyau (Yawu) a ciki , Wanda haka zai kai ga bular cuta mai wuyar magani!

-Tsaftace wuraren da ruwa ke zama, kamar su rijiyoyi, Da gulabe da dam dama, Yana kyau yan uwa musulmi mu kiyaye,'' Manzo SAW Ya hana fitsari a cikin ruwa da basu gudu '' ya hana hakan ne dan gudun kada wani ya dauki cuta daga wani ,

Musulunci yayi dukan wadannan bayanan ne dan kare lafiya dan Adam musulmai, Da kuma shari'a ta karemu daga daukar duk wasu cuttutuka,

Yaku yan uwa musulmi mu kula dan kaucewa fadawa cikin halaka Saboda ALLAH Madaukakin sarki na cewa ''KADA KU JEFA KAWUNAN KU CIKIN HALA''

Muna rokon ALLAH Yagafarta mana, Ya bamu lafiya da zama lafiya, Yayi mana saukin zafin sama da kasa dana aljihu, Ya Allah ina tawasulli da wannan khudbar ka biya mana bukatun mu, Ka gafartawa mamatan mu, Kayi jagoranci ga shuwagabanni ka dora su a turba ta dai dai.

ALHAMDULILLAH

©®‎IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA

24/Rajab/1438

21/04/2017.

AZUMIN TSOFAFFI

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌
MASALLACIN ABU HURAIRA YAR'YARA TSAFE

AZUMIN TSOFAFFI A' CIKIN WATAN RAJAB BIDI'A NE!!!!!

JAKKAR MAGORIN MUSULUNCI WALLAFAR LIMAMIN ABU HURAIRA AREA 2 TSAFE( MALAM SANI LIMAN TSAFE)

MENENE MATSAYIN AZUMIN TSOFAFFI ' SHARI'A?

ALLAH (S. W. T) YANA FADA A'CIKIN LITTAFIN SA MAI TSARKI CEWA "LALLAI ADADIN YAWAN WATANNI A' WAJEN ALLAH GOMA SHA BIYU NE (12) A' CIKIN LITTAFIN ALLAH RANAR DA AKA HALICCI SAMMAI DA KASSAI.

DAGA CIKI AKWAI 4 MASU ALFARMA, WANNAN SHI NE ADDINI MADAIDAICI. KADA KU ZALUNCI KAWUNAN KU A' CIKIN SU" ( SURATUL TAUBA AYA 25)

HADISI YA NUNA MANA CEWA WADANNAN WATANNI SUNE ( ZULQI'IDA,  ZULHIJJA,  MUHARRAM,  DA RAJAB.

ALFARMA SU KUWA ITACE  A' GIRMAMA SU DA DARAJA SU SAMA DA SAURAN WATANNIN,  SANNAN KUMA CEWA ALLAH (S. W. T) "KADA KU ZALUNCI KAWUNAN KU A' CIKIN SU " YANA NUFIN KADA KU SABI ALLAH KUMA KU KIYAYE KAWUNANKU MATUKAR KIYAYEWA A'CIKIN SU.

A' KARKASHIN WANNAN NE YA WAJABA MU JAWO HANKALIN 'YAN UWA AKAN BIDI'O DA AKEYI A' CIKIN WATAN RAJAB, WATO WATAN AZUMIN TSOFAFFI.

DAGA CIKI AKWAI SHI AZUMIN DA AKEYI, INDA ZAKA GA TSOFAFFI SUNA AZUMTAR WATAN GABA DAYA, KO SUYI RABI, KO ABINDA YAFI HAKA, KO YA KASA HAKA.

WASU MA SUNA FARA AZUMI KE NAN HAR ZUWA RANAR DA AKA GA WATAN SALLAH. TO A ZAHIRI ZA'AGA KAMAR HAKA WANI ABIN KIRKI NE, SAI DAI MU TUNA DA HADISIN DA MANZON ALLAH (S. A. W) INDA YAKE BAMU UMURNIN MU KAUCEWA DUKKAN AYYUKAN IBADA WADANDA ANNABI BAI YIBA, KUMA BAI BADA UMURNIN AYIBA, SAHABBAI BASU YIBA,  TABI'AI DA TABI'UT TABI'INA DUK BASU YI BA.

IBN  KAYYIM YA RUWAITO CEWA MANZON ALLAH (S. A. W) BAI TABA AZUMIN WATA 3. (RAJAB,  SHA'ABAN,  DA RAMADAN) A' JERE BA,     KUMA BAI TABA AZUMIN WATAN RAJAB BA,  KUMA BAISO AYI SHI BA.

IBN MAJAH YA RUWAITO CEWA MANZON ALLAH (S. A. W) YA HANA YIN AZUMIN WATAN RAJAB,

YA TABBATA CEWA SAYYIDINA ABUBAKAR (R. A) YA KYAMACI IYALIN SA SUYI AZUMIN TSOFAFFI.

  ZAMUCI GABA IN SHA ALLAHU, ALLAH YA BIYA MALAM AMIN.

AZUMIN TSOFAFFI02

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌
MASALLACIN ABU HURAIRA YAR'YARA TSAFE

           CIGABA DA KASHI NA 2.

AZUMIN TSOFAFFI A' CIKIN WATAN RAJAB BIDI'A NE!!!!!

JAKKAR MAGORIN MUSULUNCI WALLAFAR LIMAMIN ABU HURAIRA AREA 2 TSAFE( MALAM SANI LIMAN TSAFE)





MENENE MATSAYIN AZUMIN TSOFAFFI ' SHARI'A?


HAKA SHIMA SAYYIDINA UMAR (R. A) YA TSANANTA GA MASUYIN AZUMIN TSOFAFFI, IN DA HAR YAKAI YANA BULALA GA DUK WANDA YAYI IRIN WANNAN AZUMI,  HAR YANA CEWA WATAN RAJAB WATA NE WANDA JAHILAI NE KAWAI KE AZUMI A' CIKIN SA.

A' NAN MUNA JAWO HANKALIN JAMA'A AKAN WASU HADISAI DA AKE KAFA HUJJA DA SU NA YIN AZUMIN WATAN RAJAB. TO BINCIKE YA TABATAR CEWA WADANNAN HADISAI KO DAI MASU RAUNI NE, KO KUMA NA KARYA NE WADANDA BAA AIKI DA SU.

IBN HAJAR YA FADA A' CIKIN LITTAFIN SA MAI SUNA "TABAYYUNI AJABI BIMA WARADA FI FADALI RAJAB, CEWA BABU WANI INGANTACCEN HADISI WANDA YAKE NUNA FALALAR WATAN RAJAB KO YIN AZUMI A' CIKIN SA, KO YIN NAFILOLIN DARE, KO RANA A' CIKIN WATAN RAJAB.

DON HAKA DUK HADISIN DA YAZO DA FALALAR WANNAN WATAN KO DAI YA ZAMA MAI RAUNI, KO KUMA KARYA CE KAWAI. " ANNABI (S. A. W)  YACE "WANDA YA BADA WANI LABARI YACE DAGA GARENI NE,  ALHALI YASAN CEWA BA DAGA WAJENA BANE TO YA TABBATA CIKIN MANYA MAKARYATA A' DUNIYA, TO INA GA WANDA HARMA AIKATA LABARIN KARYA YAKEYI. "ALLAH YA TSARE MU AMIN.

TO DAGA WANNAN ZA'A GANE SHARRIN DA SHEDAN YAKE KULLAWA TSOFAFFI NA BATA MASU LOKACI SU, DA KARFIN SU, WAJEN YIN AZUMIN WATAN RAJAB, AMMA SAI YACE MASU SU HUTA A' CIKIN WATAN SHA'ABAN, WANDA SHINE ANNABI (S. A. W)  YAYI UMURNI A' YAWAITA AZUMI CIKIN SA.

ALLAH YA SAKAWA MALAM DA ALJANNAH BISA KOKARIN DA YAYI NA RUBUTA MANA WANNAN LITTAFI AMIN.