Saturday, 15 July 2017

MEYASA BA'A KARBA ADDU'OINMU???

🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅
*MEYASA MUKE ADDU'AH, AMMA SAI MUGA KAMAR BA'A KARBA MANA???*
🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

```An tambayu Ibrahim bn Adham(RH) akan cewa meya samemu ne, muna Addu'ah amma ba'a karba mana??

Sai yace: Zukatanku sun mutu da Abubuwa takwas(8).

NA FARKO; Munsan Allah, amma ba muyi mashi biyayya(ma'ana; munsan hakkin Allah, amma bamu gabatar mashi da hakkinshi).

NA BIYU; Muna karanta Alkur'ani, amma bamu aiki dashi(ma'ana: Bamu aiki da iyakokin da Allah ya gindaya a cikin Qur'anin).

NA UKU: Munce munason Manzon Allah (Salallahu alaihi wasallam), amma sai muka yi mashi tawaye, muka kiyin amfani da sunnar shi.

NA HUDU: Munsan cewa Shaidan makiyinmu ne, amma sai muka sakar mashi akala muna binshi.(Muna yi mashi biyayya wajen sabon Allah).

NA BIYAR: Munsan cewa Aljanna gaskiya ce, amma bamu aiki domin mu shigeta.

NA SHIDA: Munsan cewa wuta gaskiya ce, amma bamu guje mata.

NA BAKWAI: Mun wayi gari mun shagaltu da aiboban(harkokin) mutane, mu kuma mun bar namu aiboban(harkokin).

NA TAKWAS: Kun binne mataccinku, amma Baku lura da kuma wataran za'a binneku.

NA TARA: Mun ce, muna tsoron mutuwa, amma ba muyi mata tanadi ba.

NA GOMA: Muna cinye ni'imomin Allah, Amma bamu gode mashi(muna cinye abincin Allah, abin shan Allah, da sauran ni'imomi amma mun kasa gode mashi).

Wadannan da wasunsu sune dalillan dake sa muke rokon Allah sai Allah ya kyalemu da dabararmu.

Yaa Allah ka bamu ikon gode maka.
Yaa Allah ka karo mana ni'imominka ta hanyar da muka sani da wacce bamu sani ba.```

HAKKIN MALLAKA©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya(ABU SINAN)
+2348064734911
+2349030201868

SHAFUKAN SADA ZUMUNTA DOMIN BIBIYARMU.

atstsamawy@gmail.com

hashimusurajo5@gmail.com

I G @ abbansinan

http://hashimtsamiya.blogspot.com/

http://abbansinaan.blogspot.com/

http://shababusunnahtsafe.blogspot.com/

http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com/

https://mobile.facebook/hashimusurajo.tsamiya/

Saturday, 1 July 2017

GORON SALLAH

*MUHADARA MAI TAKEN; AMFANI DA KUMA ILLOLIN SOCIAL MEDIA*

   Muhadara mai taken amfani da kuma illolin social media a cikin al'umma wacce kwamitin matasa na *SHABABU AHLISSUNNAH WALJAMA'AH SUKA SHIRYA DOMIN GORON SALLAH,* muhadarar wacce *USTAZ MUSA S LAWAL(Abu salih Ibn salih)* ya gabatar a masallacin *UTHMAN BIN AFFAN TSAFE,*

Wallahi akwai abubuwan da ya kamata mu amfana dasu kwarai da gaske a cikin wannan muhadara.
Kai dai kawai shiga link dake kasa domin saukewa a wayanka.
👇👇👇👇👇👇👇👇
*Amfani da illolin social media by Ustaz musa s lawal Tsafe*

http://darulfikr.com/s/24715

Allah ya sakawa Malam da Alkhairi akan wannan lecture da yayi mana.

darulfikr.com takuce domin yada Sunnah a koda yaushe.

Copyright©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya
+2348064734911
+2349030201868

Monday, 26 June 2017

2017 RAMADAN TAFSEER

*2017 COMPLETE  RAMADAN  TAFSEER*

   COMPLETE  2017 RAMADAN  TAFSEER DAGA MASALLACIN JUMA'AH NA ABU HURAIRA AREA  II TSAFE.

  wanda Malam Sani Liman Tsafe (ABI HURAIRA)   yake gabatarwa a Area II Tsafe, jahar Zamfara  Nigeria.

Shiga  links dake kasa  Domin saukewa Cikin sauki ka saurara  Cikin kyakykyawan Sauti.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

01 Ramadan Tafseer 1438Ah Suratul Nisa i By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24378

02 Ramadan Tafseer 1438 Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24379

03 Ramadan Tafseer Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe
http://darulfikr.com/s/24380

04 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24381

05 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Sani LimanTsafe
http://darulfikr.com/s/24382

08 Ramadan Tafseer Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24383

09 Ramadan Tafseer Akan Hukunce Hukunce Mata Na Dare By Mal San Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24384

10 Ramadan Tafseer Na Dare By Abu-Hurairah Tsafe
http://darulfikr.com/s/24385

11 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24386

12 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24387

14 Ramadan Tafseer 1438 Suratul Ma ida By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24388

15 Ramadan Tafseer Na Dare Suratul Ma ida By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24389

16 Ramadan Tafseer 1438 Na Dare By Mal SaniLiman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24390

17 Ramadan Tafseer Na Dare 1438 By Mal Sani Liman Tsafe
http://darulfikr.com/s/24391

19 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24392

20 Ramadan Tafseer 1438 Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24393

21 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24394

Kasance do darulfikr.com a koda yaushe domin  samun karatuttukan maluman  sunnah.

*_Hashim Surajo Uba Tsamiya (ABU SINAAN)_*

http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com

2017 RAMADAN TAFSEER

*2017 COMPLETE  RAMADAN  TAFSEER*

   COMPLETE  2017 RAMADAN  TAFSEER DAGA MASALLACIN JUMA'AH NA ABU HURAIRA AREA  II TSAFE.

  wanda Malam Sani Liman Tsafe (ABI HURAIRA)   yake gabatarwa a Area II Tsafe, haha Zamfara  Nigeria.

Shiga  links dake kasa  Domin saukewa Cikin saki LA saurara  Cikin kyakykyawan Saudi.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

01 Ramadan Tafseer 1438Ah Suratul Nisa i By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24378

02 Ramadan Tafseer 1438 Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24379

03 Ramadan Tafseer Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe
http://darulfikr.com/s/24380

04 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24381

05 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Sani LimanTsafe
http://darulfikr.com/s/24382

08 Ramadan Tafseer Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24383

09 Ramadan Tafseer Akan Hukunce Hukunce Mata Na Dare By Mal San Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24384

10 Ramadan Tafseer Na Dare By Abu-Hurairah Tsafe
http://darulfikr.com/s/24385

11 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24386

12 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24387

14 Ramadan Tafseer 1438 Suratul Ma ida By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24388

15 Ramadan Tafseer Na Dare Suratul Ma ida By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24389

16 Ramadan Tafseer 1438 Na Dare By Mal SaniLiman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24390

17 Ramadan Tafseer Na Dare 1438 By Mal Sani Liman Tsafe
http://darulfikr.com/s/24391

19 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24392

20 Ramadan Tafseer 1438 Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24393

21 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24394

Kasance do darulfikr.com a koda yaushe domin  samun karatuttukan maluman  sunnah.

*_Hashim Surajo Uba Tsamiya (ABU SINAAN)_*

http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com

IN ANSHA RUWA...

IN ANSHA RUWA A KOMA AIKI

*IN ANSHA RUWA A KOMA AIKI!!!*

Karatun littafin NIHA YATIL ÃLAM wallafar Dr.Muhammad Abdulrahman Al-arify, karatun da *USTAZ MUSA S LAWAL TSAFE* ya fara gabatar mana a jiya SALLAH 01/10/1438AH
25/06/2017AC
Malam ya fara mana da mukaddimar littafin, kuma littafin yana magana akan alamomin tashin kiyama Manya da kanana.

Daure ka sauke wannan karatun yana da amfani matuka
👇👇👇👇👇👇👇👇
نهاية العالم د. العرفي
DAGA BAKIN; *USTAZ MUSA S LAWAL TSAFE(ABU SALIH IBN SALIH)*

http://darulfikr.com/s/24541

darulfikr.com takuce domin yada sunnah.

Copyright©
*_Hashim Sirajo Uba Tsamiya (ABU SINAN)_*

+2348064734911
+2349030201868

Saturday, 3 June 2017

HUDUBAR JUMU'AH

HUDUBAR JUMU'A
A  MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin  Massallaci Jumu'a Na Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na Liman'

Yayi Hudubar Sane Akan #TSAFTA

Godiya ta tabbata madaukakin sarki, Muna gode masa muna neman taimakonsa, Muna neman yakare daga sharrin kawunan mu,

Na shaida babu abun bautawa da gaskiya sai ALLAH Baya da abokin taraiya, Na shaida Annabi Muhammadu bawan sa ne kuma manzonsa,

Tsira da amincin ALLAH Su kara tabbata ga manzo tsira da alayen da sahabban sa da dukan wadanda suka bayan su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako!

Yan uwa musulmi a yau khudbar zatayi magana ne akan Tsafta a addinin musulunci!

Addinin musulunci yayi umarni da tsafta a kowane bangare na rayuwa, Kama daga ta jiki da kaya da dukan dai wata mu'amula ta yau da kullun,

Tsafta tana daya daga cikin umarni na farko farko da aka fara bayarwa a lokacin da musulunci yake da dumi duminsa,

Kamar yadda ALLAH Yake fada cikin suratul Muddasir cewa ''YA KAI MAI LULLUBI (Annabi Muhammad SAW) KA TASHI KAYI GARGADI KA GIRMAMA UBANGIJINKA KA TSAFTACE TUFAFIN KA''

Kunga wannan ayar tana kwadaitar damu kan tsafta, Hakama ALLAH Madaukakin sarki na cewa ''YAKU WADANDA KUKAYI IMANI IDAN KUN TSAYU GA SALLAH KU WANKE FUSKOKINKU DA KAFAFUNKU''

Yaku yan uwa musulmi kusani itafa tsafta ita ke jagoranta har mutane su soka su dinga taraiya dakai,

Yaku yan uwa musulmi daga cikin manyan ni'imomin da ALLAH Yayi mana itace ni'imar ruwan sama, Su kuwa ruwan sama suna zuwa ne dan tsaftace kasa daga datti, Da kazanta da shirka wadda shaida L.A ya qawata ma mutane yi, Kamar yadda ALLAH Madaukakin sarki yake cewa ''MUNA SAUKAR DA RUWAN SAMA DAN TSAFTACE KASA DAGA DATTI''

Yaku yan uwa musulmi tsafta tana da wani bagire a musulunci, Manzo rahama SAW Yana fada cikin wani hadisi cewa ''MAI TSAFTA ALLAH ZAI TADASHI YANA HASKE A FUSKA'' Ma'ana mai alwalla ita kuwa alwallah tsafta ce,  Hakama manzo rahama SAW Yana fada cewa ''RANAR KIYAMA AL'UMMATA ZASU ZO DA HASKE A FUSKOKIN SU DA KAFAFUN SU SABODA ALWALLAR DA SUKA AIKATA A DUNIYA''

Tsafta muhimmacinta nada matuqar yawa, shinasa sa aka alaqanta duk wata ibada da tsafta kamar su sallah, Dawafi Karatun Qur'ani da sauran ibadu,

Yana daga cikin tsafta yawaita wanka kamar su na jumu'a kamar yadda manzon rahama SAW Yake cewa ''NAYI UMARNI DA WANKAN JUMU'A''

Hakama a wata ruwayar na cewa ''WANKA JUMU'A WAJIBI NE''

Mafi yawan wasu mutane na ganin kamar tsafta batada wata alaqa da addinin musulunci, Sam ba haka bane addinin musulunci shine addinin daya fara jaddadda tsafta a duniya,

Rashin tsafta dabi'ar ce ta mushrikai, Wata rana salmanul farisi ya fito sai wani mushriki yayi mai wata magana ta izgili yana cewa ''Naga abokin (wato yana nufin annabin Muhammad SAW) ku yana umartar ku da tsafta har a makeyi''

Hakika musulunci ya sanya tsafta a ciki yanki na imani, Kamar yadda hadisin manzon Tsira yake cewa ''TSARKI SHARADI NE NA IMANI'' Kaga idan kana da kazanta to lallai imanin ka nada rauni matuka!

Saboda matsayin tsarki da tsafta yasa malaman fiqhu suke yawaita gabata da tsafta ko tsarki a farko farko,

ALLAH Madaukakin sarki ya yabi mata kan yadda suke tsafta kamar yadda yake fada a cikin suratul baqarah cewa ''LALLAI ALLAH YANA SON MASU TUBA DA MASU TSAFTA''
Ana bukatar duk bayan mata sunyi tsarki na kowane jini suyi tsarki dan tsafta su sanya turare,

Musulunci yana wajabta wasu fannona da suka zama wajibi a aikata su har guda goma sha daya (11)

1- Tsaftace baki, Ma'ana tsaftace baki ta hanyar wankewa da Brush da macling, Ko aswaki ko wani mai na goge baki, kamar yadda hadisi ya umarta cewa ''KUYI ASWAKI DAN YANA TSAFTACE BAKI DAGA KAZANTA''

2-Tsaftace suma ko gashin kai, Ma'ana tsaftace gashin kai, Ko rage sa, Ko kuma shace sa, Ko kuma askesa, Hadisi daga manzo tsira na cewa ''WANDA ALLAH YA AZURTA DA GASHI YARINGA KARRAMA GASHIN'' Ma'ana ka tsaftace shi ta dawanchan hanyoyi, Kada kabar gashin ka lalace yayi babu kyan gani ba tsafta.

3-Tsaftace gidaje da massalatai da kofar gidaje da wurare kasuwanci, Kada kubar wajen shara ta taru ko kuma yayi kasha-kasha, hadisi ya tabbata daga manzo tsira cewa ''KU TSAFTACE FARFAJIYAR KU KADA KUYI KOYI DA YAHUDAWA DAN SUNA TARA SHARA TSAKAR GIDA ''

4-SANYA TURARE Ma'ana yawan amfani da turare dan kauda wari da kazanta, Anan ma hadisi ya tabbata daga manzo tsira cewa ''LALLAI ALLAH MAI KYAU NE KUMA YANASO YAGA ANA TSAFTA''

5-Tsaftace Massallatai, Kada mubar massallatan mu babu kyau, Annabi ya gargademu da kada muje massallaci ba tsafta ''WANDA YACI ALBASA KO TAFARNUWA KADA YAZO MASSALLACI''

6- Mata masu jinin al'ada ya zama wajibi su kyautata tsafta, yana da kyau su warware kitson su, su wanke ko ina tare amfani da turare a gabansu dan inganta tsaftar su,

7-Tsaftace jiki, Mu kula da tsaftace jiki ganin yadda yanzu muke cikin lokachin zafi, Kamar yadda yagabata khudbar wancan makon

8-Kula da sunnoni goma, Manzo tsira SAW Yana cewa ''YANA CIKIN FIDDA WATO (Sunnar asali ta yan adam) sune kamar haka,
-Rage gashin baki, a kula ba askewa ake nufi ba baki daya,
-Mucika gemu, Kammala gemu ba tare aske shi ba,
-Aswaki, Yawaita aswaki yana daga cikin sunnonin asali,
-Kuskure baki, Yawaita kuskure baki idan kaji yadan yi maka nauyi,
-Rage akaifa, A yawaita rage akaifa saboda akaifa shine ne ke daukar datti ta boye a cikin hannu
-Wanke hannu, Yawaita wanke hannu, Dan gudun kada a kwaso wata cuta,
-Rage gashin hamata, Yana da kyau rage ya, Dan anan cuttutuka suke boyewa,
-Gusar da gashin mara, Hadisi yazo daga manzo tsira cewa ''KADA MUSULMI YA KUSKURA YA WUCE KWANA ARBA'IN BAI KAUDA WADANNAN KAZANTAR BA''

9-Tsaftace hanyoyin da muke bi, Mu tsaftace hanyoyin da muke bi yau da kullun, Hadisi yazo daga manzo tsira cewa ''IMANI GIDA SABA'IN NE BABBA DAGA CIKI ITACE KALMAR LA'ILAHA ILALLAH KARAMA DAGA CIKIN KUWA ITACE GUSAR DA DATTI HANYA''
Yana da kyau koda gwalab ko fitila ce a aje a hanya dan ganin haske a hanya

10-Tsaftace abinci da ruwan mu, Kiyaye ruwan sha dana koramu, Da kuma tsaftace abinci, Manzo tsira SAW Yace ''IDAN KUN SHIGA GIDA KU KULLE IDAN ZASU KWANTA KU RUFE RANDA KU KASHE WUTA KU RUFE ABINCI'' saboda shaidan baya iya buda randar da aka rufe ko abincin da aka rufe, Yana da kyau a kula, Idan ba'a rufewa shaidan zai iya zuwa ya tofa miyau (Yawu) a ciki , Wanda haka zai kai ga bular cuta mai wuyar magani!

-Tsaftace wuraren da ruwa ke zama, kamar su rijiyoyi, Da gulabe da dam dama, Yana kyau yan uwa musulmi mu kiyaye,'' Manzo SAW Ya hana fitsari a cikin ruwa da basu gudu '' ya hana hakan ne dan gudun kada wani ya dauki cuta daga wani ,

Musulunci yayi dukan wadannan bayanan ne dan kare lafiya dan Adam musulmai, Da kuma shari'a ta karemu daga daukar duk wasu cuttutuka,

Yaku yan uwa musulmi mu kula dan kaucewa fadawa cikin halaka Saboda ALLAH Madaukakin sarki na cewa ''KADA KU JEFA KAWUNAN KU CIKIN HALA''

Muna rokon ALLAH Yagafarta mana, Ya bamu lafiya da zama lafiya, Yayi mana saukin zafin sama da kasa dana aljihu, Ya Allah ina tawasulli da wannan khudbar ka biya mana bukatun mu, Ka gafartawa mamatan mu, Kayi jagoranci ga shuwagabanni ka dora su a turba ta dai dai.

ALHAMDULILLAH

©®‎IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA

24/Rajab/1438

21/04/2017.

AZUMIN TSOFAFFI

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌
MASALLACIN ABU HURAIRA YAR'YARA TSAFE

AZUMIN TSOFAFFI A' CIKIN WATAN RAJAB BIDI'A NE!!!!!

JAKKAR MAGORIN MUSULUNCI WALLAFAR LIMAMIN ABU HURAIRA AREA 2 TSAFE( MALAM SANI LIMAN TSAFE)

MENENE MATSAYIN AZUMIN TSOFAFFI ' SHARI'A?

ALLAH (S. W. T) YANA FADA A'CIKIN LITTAFIN SA MAI TSARKI CEWA "LALLAI ADADIN YAWAN WATANNI A' WAJEN ALLAH GOMA SHA BIYU NE (12) A' CIKIN LITTAFIN ALLAH RANAR DA AKA HALICCI SAMMAI DA KASSAI.

DAGA CIKI AKWAI 4 MASU ALFARMA, WANNAN SHI NE ADDINI MADAIDAICI. KADA KU ZALUNCI KAWUNAN KU A' CIKIN SU" ( SURATUL TAUBA AYA 25)

HADISI YA NUNA MANA CEWA WADANNAN WATANNI SUNE ( ZULQI'IDA,  ZULHIJJA,  MUHARRAM,  DA RAJAB.

ALFARMA SU KUWA ITACE  A' GIRMAMA SU DA DARAJA SU SAMA DA SAURAN WATANNIN,  SANNAN KUMA CEWA ALLAH (S. W. T) "KADA KU ZALUNCI KAWUNAN KU A' CIKIN SU " YANA NUFIN KADA KU SABI ALLAH KUMA KU KIYAYE KAWUNANKU MATUKAR KIYAYEWA A'CIKIN SU.

A' KARKASHIN WANNAN NE YA WAJABA MU JAWO HANKALIN 'YAN UWA AKAN BIDI'O DA AKEYI A' CIKIN WATAN RAJAB, WATO WATAN AZUMIN TSOFAFFI.

DAGA CIKI AKWAI SHI AZUMIN DA AKEYI, INDA ZAKA GA TSOFAFFI SUNA AZUMTAR WATAN GABA DAYA, KO SUYI RABI, KO ABINDA YAFI HAKA, KO YA KASA HAKA.

WASU MA SUNA FARA AZUMI KE NAN HAR ZUWA RANAR DA AKA GA WATAN SALLAH. TO A ZAHIRI ZA'AGA KAMAR HAKA WANI ABIN KIRKI NE, SAI DAI MU TUNA DA HADISIN DA MANZON ALLAH (S. A. W) INDA YAKE BAMU UMURNIN MU KAUCEWA DUKKAN AYYUKAN IBADA WADANDA ANNABI BAI YIBA, KUMA BAI BADA UMURNIN AYIBA, SAHABBAI BASU YIBA,  TABI'AI DA TABI'UT TABI'INA DUK BASU YI BA.

IBN  KAYYIM YA RUWAITO CEWA MANZON ALLAH (S. A. W) BAI TABA AZUMIN WATA 3. (RAJAB,  SHA'ABAN,  DA RAMADAN) A' JERE BA,     KUMA BAI TABA AZUMIN WATAN RAJAB BA,  KUMA BAISO AYI SHI BA.

IBN MAJAH YA RUWAITO CEWA MANZON ALLAH (S. A. W) YA HANA YIN AZUMIN WATAN RAJAB,

YA TABBATA CEWA SAYYIDINA ABUBAKAR (R. A) YA KYAMACI IYALIN SA SUYI AZUMIN TSOFAFFI.

  ZAMUCI GABA IN SHA ALLAHU, ALLAH YA BIYA MALAM AMIN.

AZUMIN TSOFAFFI02

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌
MASALLACIN ABU HURAIRA YAR'YARA TSAFE

           CIGABA DA KASHI NA 2.

AZUMIN TSOFAFFI A' CIKIN WATAN RAJAB BIDI'A NE!!!!!

JAKKAR MAGORIN MUSULUNCI WALLAFAR LIMAMIN ABU HURAIRA AREA 2 TSAFE( MALAM SANI LIMAN TSAFE)





MENENE MATSAYIN AZUMIN TSOFAFFI ' SHARI'A?


HAKA SHIMA SAYYIDINA UMAR (R. A) YA TSANANTA GA MASUYIN AZUMIN TSOFAFFI, IN DA HAR YAKAI YANA BULALA GA DUK WANDA YAYI IRIN WANNAN AZUMI,  HAR YANA CEWA WATAN RAJAB WATA NE WANDA JAHILAI NE KAWAI KE AZUMI A' CIKIN SA.

A' NAN MUNA JAWO HANKALIN JAMA'A AKAN WASU HADISAI DA AKE KAFA HUJJA DA SU NA YIN AZUMIN WATAN RAJAB. TO BINCIKE YA TABATAR CEWA WADANNAN HADISAI KO DAI MASU RAUNI NE, KO KUMA NA KARYA NE WADANDA BAA AIKI DA SU.

IBN HAJAR YA FADA A' CIKIN LITTAFIN SA MAI SUNA "TABAYYUNI AJABI BIMA WARADA FI FADALI RAJAB, CEWA BABU WANI INGANTACCEN HADISI WANDA YAKE NUNA FALALAR WATAN RAJAB KO YIN AZUMI A' CIKIN SA, KO YIN NAFILOLIN DARE, KO RANA A' CIKIN WATAN RAJAB.

DON HAKA DUK HADISIN DA YAZO DA FALALAR WANNAN WATAN KO DAI YA ZAMA MAI RAUNI, KO KUMA KARYA CE KAWAI. " ANNABI (S. A. W)  YACE "WANDA YA BADA WANI LABARI YACE DAGA GARENI NE,  ALHALI YASAN CEWA BA DAGA WAJENA BANE TO YA TABBATA CIKIN MANYA MAKARYATA A' DUNIYA, TO INA GA WANDA HARMA AIKATA LABARIN KARYA YAKEYI. "ALLAH YA TSARE MU AMIN.

TO DAGA WANNAN ZA'A GANE SHARRIN DA SHEDAN YAKE KULLAWA TSOFAFFI NA BATA MASU LOKACI SU, DA KARFIN SU, WAJEN YIN AZUMIN WATAN RAJAB, AMMA SAI YACE MASU SU HUTA A' CIKIN WATAN SHA'ABAN, WANDA SHINE ANNABI (S. A. W)  YAYI UMURNI A' YAWAITA AZUMI CIKIN SA.

ALLAH YA SAKAWA MALAM DA ALJANNAH BISA KOKARIN DA YAYI NA RUBUTA MANA WANNAN LITTAFI AMIN.

Monday, 22 May 2017

AZUMIN WATAN RAMADHANA

🍇🍉🍇🍉🍇🍉🍇🍉🍇🍉
*AZUMIN WATAN RAMADANA*
🍉🍇🍉🍇🍉🍇🍉🍇🍉🍇

*بسم الله الرحمن الرحيم*

_Rubutawa;_ *HASHIM SURAJO UBA(ABU SINÃN)*

```ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU.

  Godiya ta tabbata ga Allah s.w.t shi kadai Wanda yayi mana umurni da azumtar ramadana, tsira da amincin Allah su tabbata ga farin jekada, Annabi Muhammad s.a.w Wanda ya koya mana yadda zamu gabatar da ibadar azumi da sauran ibadoji.

Bayan haka;

FALALAR WATAN RAMADANA DA AZUMI A CIKIN WATAN.

Manzon Allah s.a.w yace; "idan ramadana ya shigo, ana bude kofofin sama, ana kulle kofofin jahannama, ana daure shaidanu.
A wani hadisin kuwa manzon Allah s.a.w cewa yayi" Dukkan wani aiki da dan Adam zaiyi, ana lunka aikin da lada goma irinsa, idan a ramadana ne, ana lunkashi zuwa lunki (700), sai Allah mai girma da daukaka yace ;  banda azumi, domin azumi nawa ne, kuma ni zan sakawa Wanda yayi shi, yabar matarshi da abubuwan da yakeso, da abinci, da abin sha saboda ni, mai azumi Nada farin ciki biyu, farin ciki lokacin buda baki (shan ruwa) da farin ciki lokacin haduwarshi da Allah, yamin/warin bakin mai azumi yafi turaren almiski kamshi a wurin Allah.[Bukhari da Muslim]

ABUBUWAN DA SUKA WAJABA GAREKA A RAMADANA

Ya dan uwa

Kasani cewa Allah ya wajabta mana azumi domin mu bauta masa dashi, sannan kuma ya kasance cewa azuminka ya zamto karbabbe mai amfani.
Dole ne ka kiyaye wadannan abubuwan da zasu zo domin samun cikakkar lada;

1- kiyaye sallah; Da yawa daga cikin masu azumi suna wasa da sallah, bayan kuwa cewa tana daga cikin gimshikan addini, barinta kuma yana kai mutum ga kafurci.

2- Dole ka kasance mai kyawawan dabi'u; Dole ne mu tsoraci kafurci da zagin addini, da aikata muna nan dabi'u a cikin mutane, kafirci yana fitar da musulmi daga addini.

3- Dole ne mu kiyaye halshenmu da sukar juna.
 
Manzon Allah s.a.w yana cewa; "idan dayanku yana azumi, to kada ya fadi maganganun da basu dace ba, idan wani ya zageka ko ya nemi yayi fada da kai, sai kace mashi ni azumi Nike, ni azumi Nike.

4- Ka nisanci zuwa wurin da ake aikata barna! Ko kallon fina-finai na banza, domin hakan zai kai ga bata azuminka.

5- Ka yawaita sadaka ga makusantanka da mabukata, da ziyartar yan uwanka.

6- Ka yawaita zikiri da karatun Qur'ani da saurararshi, da bibiyar ma'anoninsa, da aiki da karantar warshi, sannan da zuwa masallatai domin daukar darussa masu amfani, kamar sauraran tafsirai, yin i'itikafi a masallaci idan goman karshe na ramadana suka kama.

7- karanta takardu akan azumi, domin sanin hukunce- hukuncen da suka shafi azumi, ta yarda zakasan cewa cin abinci ko abin sha da mantuwa baya karya azumi, kasan cewa ita janaba wacce ta sameka da daddare bata hana ka daukar azumi da sauransu.

LADUBBAN DA SUKA SHAFI AZUMI.

1- kiyaye halshe; Manzon Allah s.a.w yace; "Duk Wanda bai bar zancen karya ba, da aiki da zancen karya, Allah baya da bukatar barin cinsa ko shansa.

2- BUDA BAKI DA SAHUR DA ADDU'AH.

Manzon Allah s.a.w yace; "idan dayanku zaiyi buda baki, to ya fara da dabino domin akwai albarka a ciki, idan bai samu dabino ba toh sai yayi da ruwa, domin suna tsalkakewa.
Manzon Allah s.a.w ya kasance idan zaiyi buda baki yana fadar;
ذهب الظمأ، وابتلت العروق، وثبت الأجر، إن شاء الله.

Ma'ana: "YUNWA TA TAFI, GABOBI SUN DAI DAI TA, LADA TA TABBATA DA YARDAR ALLAH".
Manzon Allah s.a.w yace; "mutane baza su gushe suna samun alkhairi ba matukar suna gaggauta buda baki.

Anan dole mu gujewa muna nan akeedun shi'ah wadanda basa shan ruwa sai duhu ya shigo sosai, suna kafa hujja da ayar Qur'ani dake cikin suratul bakara, inda Allah s.w.t yake cewa; "...sannan Ku cika azumi zuwa dare. Wanman magana malamai sunyi bayanin me ake nufi tun da dadewa, mai Neman Karin bayani ya duba tafsirin "Aisarat-tafaseer, na jabir jaza'iry."

Manzon Allah s.a.w yace"kuyi sahur, domin a cikin yin sahur akwai albarka."

Manzon Allah s.a.w yace"Duk Wanda ya ciyar da mai azumi, yana da kwatan kwacin ladarsa, ba tare da an rage komai daga ciki ba.

3-  DAGA CIKIN FA'IDOJIN AZUMI

   Duk Wanda yayi azumin ramadana, yana mai imani da Neman lada, an gafarta mashi abunda ya gabata na zunubbansa.

Duk Wanda yayi tsayuwar ramadana, yana mai imani da Neman lada, an gafarta mashi zunubbansa.(ma'ana: tsayuwar tarawihi da kiyamul-laili.)

4- WADANDA AKA YIWA RANGWAMEN AZUMI.

   *Marar lafiya da matafiyi, zasu ranka saboda fadar Allah s.w.t cewa;"Wanda ya kasance a cikinku marar lafiya ko akan hanyar tafiya, zai ranka azumin a kwanakin sauran watanni."
Amma marar lafiya Wanda ba'asa ran warkewa a kusa, toh sai ya rinka ciyar da talaka daya a kowace rana.

* Mai haila, da jinin haihuwa zasu aje azumi, saboda fadar ummuna Aisha R.A; "mun kasance ana umurtanmu da ranka azumi, amma ba'a umurtanmu da ranka sallah.[Bukhari da Muslim].

* Dattijo da dattijiya, wadanda sun tsufa sosai basa iya daukar azumi toh zasu ciyar da talaka daya a kowace rana.

* Mace mai ciki da mai shayarwa idan sunji tsoron rayukansu, toh zasu aje azumi sannan su ranka kawai, amma idan suna jin tsoron yayansu ne kawai, toh zasu ranka kuma su ciyar.

5- ABUBUWAN DAKE BATA AZUMI.

Abubuwan dake bata azumi sun kasu gida biyu:
Na farko; Abunda ke bata azumi Wanda ke wajabta rankawa kawai;

* Cin abinci ko abinsha da gangan.

* Yin amai da gan gan, saboda fadar annabi Muhammad s.a.w cewa: " Duk Wanda yayi amai, toh zai ranka azumi.[Hakim ya ruwaito]

* Mace mai haila da mai haihuwa, koda sauran mintuna kadan ayi buda baki tazo musu, toh zasu ranka azumin.

* Istimna'i(masturbation) wasa da al'aura da hannunka har maniyyi ya fito shima yana bata azumi kuma sai ka ranka.

Abu na biyu dake bata azumi kuma yake wajabta ranko da kaffara shine JIMA'I, akan maganar malamai kaffarar shine yanta baiwa ko azumin kwana sittin(60) a Jere.

6- ABUBUWAN DA BASU BATA AZUMI

* Cin abinci ko abinsha da mantuwa, ko da kuskure ko da tilasci! Babu ranko kuma babu kaffara, saboda fadar manzon Allah s.a.w cewa"Wanda ya manta yana azumi ya ci ko ya sha toh ya cika azuminsa, Allah ne ya ciyar dashi kuma ya shayar dashi.[Bukhari da Muslim]

* Amai ba dagan gan ba.

* Yin aswaki a kowane lokaci ko brush da sauransu.

* Dandana abinci da sharadin kada ka bari ya wuce maka.

* Sumbantar matarka, da sharadin kada akai ga aikata jima'i. Saboda manzon Allah s.a.w ya kasance yana sumbantar Aisha alhali yana azumi[Bukhari da Muslim].

* Cirewar hakori, ko zubar jini daga baki ko hanci.

* idan Alfijir ya keto alhali abunsha na hannunka, kada ka aje har sai ka biya bukatarka.

*jinkirta wankan janaba ko haila ko na haihuwa daga dare zuwa hudowar alfijir. Abunda yafi shine ayi gaugawar yi kafin sallar asuba.

Muna rokon Allah ya amfanar damu da abunda muka rubuta, Allah yasa munyi domin Neman yardar shi, Allah ya sanya ibadojin da zamu gabatar a ramadana su zamo karbabbu, kuma su zamo sanadiyyar tsira garemu duniya da lahira. Inda mukayi kuskure Allah ya shefeshi daga idanun masu karatu ya fahimtar dasu tare damu gabaki daya. Allah ya doramu akan tafarki madaidaici.

WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.

COPYRIGHT©
Hashim Surajo Uba(ABU SINÃN)```

http://hashimtsamiya.blogspot.com

http://abbansinaan.blogspot.com

http://abbansinan.wordpress.com

http://shababusunnahtsafe.blogspot.com

http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com

atstsamawy@gmail.com

+2348064734911
+2348064734911

DABI'UN MAGABATA A CIKIN WATAN RAMADHANA

🍌🍌🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍌🍌
*DABI'UN MAGABATA A CIKIN WATAN RAMADANA*
🍇🍇🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍇🍇

_Rubutawa;_ *Hashim Ibn Surajo Ibn Uba(ABU SINÃN)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

```Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.

Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai Wanda yayi umurni da azumtar watan ramadana, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad s.a.w, Wanda ya koya mana yanda zamu gabatar da azumin.

Bayan haka;

Magabata suna da wasu dabi'u da ayuka da zantuka a cikin ramadana, watan ramadana shine watan da Allah s.w.t ke cewa; "watan ramadana Wanda q cikinshi ne aka saukar da Qurani, domin shiriya ga mutane, da kuma bayanai game da shiriyar....[bakara 185]

Magabata na kwarai suna da ayukan da suke aikatawa a ramadana  fiye da sauran watanni.  Daga cikin magabatan akwai;
*IMAMU MALIK IBN ANAS(imamu darul hijra) ya kasance baya dakatar da karatuka a masallacin Annabi Muhammad s.a.w sai a ramadana, domin yana shagaltuwa da karatun Qurani ne kawai.

*SUFYANUS-THAURY R.H; ya kasance idan Ramadana ya shigo, yana barin dukkan wasu ibadodi, yana shagaltuwa da tilawar Qur'ani.

* MUHAMMAD IBN ISMA'IL AL-BUKHARI(mai sahihul-bukhari): ya kasance a cikin duk yini daya yana sauke Qur'ani, yana tsayuwar tarawihi acikin kwana uku na tqrawihin yana sauke Quran.

*SA'ID IBN JUBAIR: ya kasance yana saukar Qur'an a duk kwana biyu.

* ABU AWANAH yace; naga IMAMU QATADA yana karantar da Qur'an a watan ramadana.

*IMAMU QATADA; ya kasance yana saukar Qur'ani a duk bayan kwana bakwai, idan ramadana ya shigo yana sauka duk kwana uku, idan kwanaki goma na karshe suka shigo yana saukewa a kowane dare.

*RABEEY IBN SULAIMAN(Dalibin imamush-shafi'i) R.H yana cewa; imamush-shafi'i ya kasance yana saukar Qur'ani a ramadana sau sittin (60)[kowace rana sau biyu] a kowane wata yana sauka sau talatin(30) bayan ramadana.

    Kiyamul-laili aikin Annabi Muhammad s.a.w da sahabbansa ne, Aisha R.A take cewa; "kada kubar tsayuwar dare, domin Manzon Allah s.a.w bai taba barinta ba, idan baya lafiya yana yi a zaune.

* Umar Ibn khaddab R.A ya kasance yana sallar dare dai dai gwargwado, idan dare ya raba, said ya tayar da iyalansa domin yin sallar, yana cewa SALLAH! SALLAH!! SALLAH!!! Sannan sai ya karanto aya ta 132 dake cikin suratu Daha, inda Allah madaukakin sarki yake cewa; "Ka umurci iyalanka da yin SALLAH ka kwadaitar dasu akanta, bamu tambayarka wani arziki mine masu azurtaka....

  Wannan shine dabi'un magabata na kwarai a watan ramadana, to mu ya halinmu yake a wannan wata mai albarka???

* Abdullahi Ibn umar(Allah ya kara masu yarda) ya kasance yana yin azumi ba ya buda baki(shan ruwa) sai tare da talakawa, ya kasance idan yana cin abinci sai wani mabukaci yazo ya tambaya sai ya tashi daga abincin ya mika masa, ya wuce da azumi ba tare da yayi sahur ba.

  Wadannan sune magabata na kwarai, kuzo Mani da irinsu a wannan zamanin yã Ku masu da'awar salafiyya da Sunnah!?

*YUNUS IBN YAZEED yake cewa; IBN SHIHAB AZ-ZUHURY ya kasance idan ramadana ya shigo yana cewa; "Wannan watan Qur'ani ne, da kuma ciyar da abinci".

* HAMMAD IBN ABI SULAIMAN ya kasance yana ciyar da mutum dari biyar(500) a watan ramadana. Ya kasance kuma yana ba kowane dayansu dirhami Dari(100).

  Yã yan uwa na masu daraja ya kamata mu kwatanta rabin abunda magabatanmu na kwarai suka aikata na ayukan alkhairi, kada mu shagaltu da abunda bazai amfanemu ba, daga baya mu koma da na sani! Allah madaukakin sarki yana cewa;"ومن أعرض عن ذكري فإن له معيشة ضنكا ونحشره يوم القيامة أعمى، قال رب لم حشرتني أعمى وقد كنت بصيرا، قال كذلك أتتك آياتنا فنسيتها وكذلك اليوم تنسى، وكذلك نجزي من أسرف ولم يؤمن بآيات ربه، ولعذاب الآخرة أشد وأبقى.

Allah yq karemu.

WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.



COPYRIGHT©
Hashim Ibn Surajo Ibn Uba(ABU SINÃN)```

atstsamawy@gmail.com

http://hashimtsamiya.blogspot.com

http://abbansinaan.blogspot.com

http://abbansinan.WordPress.com

http://shababusunnahtsafe.mywapblog.com

http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com

+2348064734911
+2349030201868

YAYA ZAMU FUSKANCI RAMADHANA???

🍌🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍌
*YA YA ZAMU FUSKANCI RAMADANA???*
🍇🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍇

_Rubutawa:_ *Hashim Ibn Siraj Ibn Uba{ABU SINÃN}*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

```Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai Wanda ya wajabta mana yin azumin watan ramadana, Tsira da amincin Allah su tabbata ga farin jekada  Annabi Muhammad s.a.w Wanda ya koya mana yadda zamu gabatar da azumin ramadana.

Bayan haka;

Allah s.w.t yana fada a cikin suratul bakara aya ta 185 cewa;" watan ramadana Wanda a cikinsa ne aka saukar da Qur'ani domin shiriya ga mutane da kuma bayyanar da shiriyar....."

Ya yan uwa

Allah s.w.t ya kebance watan ramadana da kebantattun abubuwa masu yawa akan waninsa. Daga cikin abubuwan akwai;

* Fadar manzon Allah s.a.w cewa: warin bakin mai azumi, yafi turaren almiski kamshi a wurin Allah.
* Mala'iku na nemawa mai azumi gafara har zuwa lokacin da zaiyi buda baki.
* Ana tsare shaidanu a cikin Ramadana.
* Ana bude kofofin aljanna, ana rufe kofofin wuta.
* A cikin Ramadana ne Daren lailatul kadri yake, wadda tafi wata dubu Alkhairi.
* Allah na gafartawa mai azumi a karshen daren ramadana.

Ya yan uwa
Da wane irin abu zamu tarbi ramadana? Da wasannin banza??? Ko da zuwa kallon kwallo??? Ko da kallon fina finai???
Muna neman Allah ya tsaremu da aikata daya daga cikinsu a wannan wata mai albarka.

Shi bawan Allah na kwarai yana fuskantar ramadana da tuba zuwa ga Allah, yana mika lokuttanshi gaba daya domin yin ayukan kwarai, bawan Allah na kwarai shine mai rokon Allah akan ya karba masa ibadojinsa da addu'oinsa.

1- AZUMI

Manzon Allah s.a.w yana cewa; "Dukkan wani aiki da mutum zai yi, yana da ladar goma irinsa, amma ga azumi ana lunka aikin zuwa lunki dari bakwai(700). Allah mai girma da daukaka yace; banda azumi! Azumi nawa ne, kuma ni zan sakawa masu azumi,(ma'ana babu Wanda yasan adadin ladar mai azumi sai Allah) sun bar abubuwan da suke sha'awa da kauna, sun bar abinci da abin sha saboda ni, mai azumi nada farin ciki biyu, farin ciki lokacin buda baki(shan ruwa), da kuma farin ciki lokacin haduwarsa da ubangijinshi. Warin/yamin bakin mai azumi yafi turaren almiski kamshi a wurin Allah.[Bukhari da Muslim]

Manzon Allah s.a.w yace; "Duk Wanda ya azumci ramadana, yana mai imani, da kwadayin Neman lada, an gafarta mashi abunda ya gabata na zunubbanshi.[Bukhari da Muslim]
2- SALLAR TARAWIHI/KIYAMUL-LAILI.

Manzon Allah s.a.w yace; "Duk Wanda yayi tsayuwa a ramadana, yana mai kwadayin Neman lada, an gafarta mashi abunda ya gabata na zunubanshi.[Bukhari da Muslim]

3- SADAKA
Manzon Allah s.a.w ya kasance yafi kowa sadaka a Ramadana da waninsa, manzon Allah kyautarsa tafi iskan dake kadawa yawa, domin tana game kowa da kowa. Manzon Allah s.a.w ya kasance yana cewa; "Mafificiyar sadaka, itace wacce akayi a cikin Ramadana.

4- CIYAR DA ABINCI

Akwai alkhairai kwarai da gaske a cikin ciyar da abinci, a Ramadana ne ko waninsa. Kamar yadda Allah s.w.t ya ambata siffofin mutanen kirki a cikin suratul insãn aya ta 8-12 saboda suna ciyar da abinci tare da zukatansu na cikin jin dadi da walwala lokacin da suke ciyarwar.
Magabata na kwarai sun kasance suna ciyar da abinci a ramadana kwarai da gaske, manzon Allah s.a.w yana cewa; "yã Ku mutane Ku watsa sallama, Ku ciyar da abinci, Ku sadar da zumunta, kutashi lokacin da mutane ke barci domin kuyi sallah, zaku shiga aljanna da aminci.[imamu Ahmad ya ruwaito da tirmidhi, Albany ya ingantashi].
Manzon Allah s. a.w yace: "Duk Wanda ya ciyar da mai azumi, yana da kwatan kwacin ladarsa, ba tare da anrage mashi komai ba.[imamu Ahmad ya fitar, da nasa'i, Albany ya ingantashi.

5- NEMAN LAILATUL-KADRI.
Allah madaukakin sarki yana cewa: "Lallai mu muka saukar dashi (Qur'ani) a daren daraja, wa ya sanar dakai me ake cewa daren daraja, daren daraja yafi Alkhairi fiye da wata dubu.
Manzon Allah s. a.w yace; "Duk Wanda yayi tsayuwar daren lailatul-kadri, yana mai imani da kwadayin Neman lada, an gafarta mashi zunubbansa.[Bukhari da Muslim]

Lailatul-kadari ana nemanta a daren 21,23,25,27 ko 29. Hadisi ya tabbata daga  ummuna Aisha R.A tacewa manzon Allah s.a.w idan na dace da daren lailatul-kadari me zan fada? Sai yace mata kice; اللهم إنك عفو،تحب العفو،فعف أني
Ma'ana; "yã Allah kai mai yafiya ne, kanason masu yafiya, ka yafe mani.[Ahmad ya ruwaito da tirmidhi, Albany ya ingantashi].

6- YAWAITA ZIKIRI DA ADDU'AH DA ISTIGFARI.

Ya yan uwa
  Kwanakin watan ramadana masu tsada ne, mu daure mu ribacesu da yawaita zikiri da addu'ah, musamman a kebantattun lokuta na amsar addu'ah. Daga cikin lokuttan akwai;
* Lokacin da mai azumi zaiyi buda baki, ba'a maida addu'ah a wannan lokacin.

*  Daya bisa ukun dare, lokacin da Allah s.w.t yake saukowa yana cewa: "ina mai rokona in amsa mashi, ina mai neman gafara in gafarta mashi.

Daga karshe ina kwadaitar damu akan mu tsaya mu ribaci wannan wata mai albarka kafin ya wuce! Idan ya wuce bamu da tabbacin zamu kara riskarshi.

Allah ya tabbatar damu akan aikata abubuwan da suka dace da sunnah a cikin wannan wata mai albarka.

        WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.



COPYRIGHT©
Hashim ibn Surajo ibn Uba(ABU SINÃN)
ATS~TSAMAWY```

atstsamawy@gmail.com

http://hashimtsamiya.mywapblog.com

http://abbansinaan.mywapblog.com

http://abbansinan.WordPress.com

http://shababusunnahtsafe.mywapblog.com

http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com

https://free.facebook.com/hashimusurajo.tsamiya

+2348064734911
+2349030201868

Wednesday, 19 April 2017

AZUMIN WATAN RAJAB(AZUMIN TSOFAFFI) SUNNAH NE KO BIDI'AH???

🌺🍇🍏🌹🌷🌼🌸💐🌺
*AZUMIN WATAN RAJAB(AZUMIN TSOFAFFI) SUNNAH NE KO BIDI'AH???*
🌺💐🌸🌼🍇🌷🌹🍏🌺

(001)

Rubutawa: *_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*

بسم الله الرحمن الر حيم

```Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya chanchanci a bauta masa shi kadai kuma ya hanemu da shirkah, Tsira da Aminci su tabbata ga farin jekada Annabi Muhammad s.a.w wanda ya tsoratar damu daga aikata bidi'ah.

Bayan haka; Nayi nufin yin wannan rubutu ne saboda ganin ya dace mu fadakar da yan uwa musamman iyaye da kakanni da ake zalunta da hadissan karya, dangane da falalar watan Rajab.

Da farko dai shi watan Rajab yana daya daga watanni masu alfarma wanda aya ta 36a suratu taubah tayi bayani.

✏✏✏✏✏✏✏✏
MAGANGANUN MAGABATA AKAN AZUMIN WATAN RAJAB(AZUMIN TSOFAFFI)
✏✏✏✏✏✏✏✏

kai tsaye yanzu ga Wata tambaya da akayi ma sheikh bin baaz(R.H) dangane da azumin Rajab(azumin tsofaffi).

An tambayi sheikh bin baaz(R.H) akan cewa shin ko yana halatta azumtar watan Rajab (AZUMIN TSOFAFFI) gaba dayansa? Domin wasu Malamai suna fadar cewa: duk wanda ya azumci Rajab, an gafarta mashi zunubbansa koda sun kai yawan kumfar teku, wasu kuma malaman sunyi hani da azumtar watan suna cewa; duk da zamanshi cikin watanni masu alfarma baya halatta a azumceshi baki daya???

Ga amsar da bin baaz ya bada, yana cewa; " Abun sani kawai shine ba'a shar'anta azumtar watan Rajab ba! Bari ma an karhantashi, abunda ya tabbata shine an shar'anta azumin sha'aban, manzon Allah s.a.w ya kasance yana yin azumin sha'aban, yana azumyar sha'aban sai kadan yake  ragewa, amma Rajab an karhanta yin azumi a cikinsa, azumi a cikinsa yana daga cikin aikin jahiliyya, saboda masu azumtar basu da dalilin azumtar watan!!! Hadisan da ake yawo dasu akan falalar watan Rajab basu da asali, bari ma na karya ne wadanda basu inganta ba, abunda shari'ah ta shar'anta ga musulmai shine suci susha a watan Rajab, sai dai idan ya kasance kana yin azumin nafila tun kafin zuwan watan wanda su dama shari'ah ta tabbatar dasu, kamar; litinin da Alhamis, Ayyamul-beedh da sauransu, wannan yana da kyau kuma babu laifi, amma azumtar watan gaba dayansa, ko kuma baka saba yin azumin nafila ba sai da watan ya shigo sai ka fake da azumin nafila ka gabatar da na Rajab wannan shari'ah bata yadda dashi ba.
Wannan itace amsar da sheikh bin Baaz ya bada dangane da azumin tsofaffi na Rajab.

Hadisi ya tabbata daga Aisha matar Annabi Muhammad s.a.w tana cewa:كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يصوم حتى نقول لايفطر، ويفطر حتى نقول لايصوم، وما رأيته أكثر صياما منه في شعبان.
[صحيح أخرجه البحاري(١٩٦٩)، و مسلم(١١٥٦)].

Ma'ana; Aisha R.A take cewa; "Manzon Allah s.a.w ya kasance yana yin azumi har sai nace bai cin abinci! Yana cin abinci har sai nace bai yin azumi(ma'ana yana yin azumi da yawa, haka kuma yana aje azumi ya huta sosai) ban taba ganin Manzon Allah s.a.w yana cika azumin wata daya ba sai dai idan ramadhan ne, ban taba ganin watan da yafi azumi a cikinsa ba face sha'aban.
[Bukhari da Muslim].

ﻗﺎﻝ ﺷﻴﺦ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ
" ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ " ‏( 25/290 ‏) :
" ﻭﺃﻣﺎ ﺻﻮﻡ ﺭﺟﺐ ﺑﺨﺼﻮﺻﻪ ﻓﺄﺣﺎﺩﻳﺜﻪ ﻛﻠﻬﺎ
ﺿﻌﻴﻔﺔ ، ﺑﻞ ﻣﻮﺿﻮﻋﺔ ، ﻻ ﻳﻌﺘﻤﺪ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻋﻠﻰ
ﺷﻲﺀ ﻣﻨﻬﺎ ، ﻭﻟﻴﺴﺖ ﻣﻦ ﺍﻟﻀﻌﻴﻒ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﺮﻭﻯ ﻓﻲ
ﺍﻟﻔﻀﺎﺋﻞ ، ﺑﻞ ﻋﺎﻣﺘﻬﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﺿﻮﻋﺎﺕ ﺍﻟﻤﻜﺬﻭﺑﺎﺕ...

Shaikhul Islam Ibn taimiyyah (RH) y
ace: “Kebance watan rajab da yin azumi,
dukkan hadisan
da su ka zo akan haka da’ifai ne (masu
rauni), bari
ma hadisan karya ne, masu ilimi
basu amfani dasu, domin basu
cikin hadisan
da ake amfani dasu don nuna falalar
aikata abu,  bari ma dukkan su ma
hadisai ne
na karya..”
Duba Majmu’u Fatawa (25/290).

ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
" ﻛﻞ ﺣﺪﻳﺚ ﻓﻲ ﺫﻛﺮ ﺻﻴﺎﻡ ﺭﺟﺐ ﻭﺻﻼﺓ ﺑﻌﺾ
ﺍﻟﻠﻴﺎﻟﻲ ﻓﻴﻪ ﻓﻬﻮ ﻛﺬﺏ ﻣﻔﺘﺮﻯ " ﺍﻧﺘﻬﻰ ﻣﻦ " ﺍﻟﻤﻨﺎﺭ
ﺍﻟﻤﻨﻴﻒ " ‏(ﺹ 96 ‏)

Imam Ibnul Qaiyim (RH) y ace;
“Dukkan hadisan
da suka ambaci azumin watan rajab da
sallatar wasu
darare a cikin sa, hadisai ne na karya kuma
kirkirarru”.
Duba Almanarul Muniif (shafi 96).

ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺤﺎﻓﻆ ﺍﺑﻦ ﺣﺠﺮ ﻓﻲ " ﺗﺒﻴﻴﻦ
ﺍﻟﻌﺠﺐ " ‏(ﺹ 11 ‏) :
" ﻟﻢ ﻳﺮﺩ ﻓﻲ ﻓﻀﻞ ﺷﻬﺮ ﺭﺟﺐ , ﻭﻻ ﻓﻲ ﺻﻴﺎﻣﻪ
ﻭﻻ ﺻﻴﺎﻡ ﺷﻲﺀ ﻣﻨﻪ ﻣﻌﻴﻦ , ﻭﻻ ﻓﻲ ﻗﻴﺎﻡ ﻟﻴﻠﺔ
ﻣﺨﺼﻮﺻﺔ ﻓﻴﻪ ﺣﺪﻳﺚ ﺻﺤﻴﺢ ﻳﺼﻠﺢ ﻟﻠﺤﺠﺔ "
ﺍﻧﺘﻬﻰ.

Alhafiz Ibn Hajar Al-Asqalani yake
cewa; “Babu
wani abu da aka ruwaito na falalar
watan Rajab,
ko yin azumi a cikin sa, ko azumtar
wasu adadin
kwanaki ayyanannu, ko tsayuwar
wasu darare
kebantattu”.
Duba Tabyinul Ajab (shafi 11).

ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺳﻴﺪ ﺳﺎﺑﻖ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ " ﻓﻘﻪ
ﺍﻟﺴﻨﺔ " ‏( 1/383 ‏) :
" ﻭﺻﻴﺎﻡ ﺭﺟﺐ ﻟﻴﺲ ﻟﻪ ﻓﻀﻞ ﺯﺍﺋﺪ ﻋﻠﻰ ﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ
ﺍﻟﺸﻬﻮﺭ , ﺇﻻ ﺃﻧﻪ ﻣﻦ ﺍﻷﺷﻬﺮ ﺍﻟﺤﺮﻡ , ﻭﻟﻢ ﻳﺮﺩ ﻓﻲ
ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ ﺃﻥ ﻟﻠﺼﻴﺎﻡ ﻓﻀﻴﻠﺔ ﺑﺨﺼﻮﺻﻪ ,
ﻭﺃﻥ ﻣﺎ ﺟﺎﺀ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﻣﻤﺎ ﻻ ﻳﻨﺘﻬﺾ ﻟﻼﺣﺘﺠﺎﺝ ﺑﻪ
" ﺍﻧﺘﻬﻰ

Imam Sayyid Sabiq (RA) yake cewa;
“Azumin
watan rajab bashi da wani fifiko na
falala akan
waninsa cikin watanni, sai dai shi
yana daga cikin
watanni (guda hudu) ma su alfarma,
kuma ba a
samu a cikin sunnah ingatacciya ba cewa
yin azumi a
cikin sa yana da falala kebantacciya,
abunda ya zo
akan haka (ma’ana hadisan da suka
zo) ba a kafa
hujja dasu (domin da’ifai ne)”
Duba Fiqhus-Sunnah (1/383).

ﻭﺳﺌﻞ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻦ ﺻﻴﺎﻡ
ﺍﻟﺴﺎﺑﻊ ﻭﺍﻟﻌﺸﺮﻳﻦ ﻣﻦ ﺭﺟﺐ ﻭﻗﻴﺎﻡ ﻟﻴﻠﺘﻪ .
ﻓﺄﺟﺎﺏ :
" ﺻﻴﺎﻡ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺴﺎﺑﻊ ﺍﻟﻌﺸﺮﻳﻦ ﻣﻦ ﺭﺟﺐ ﻭﻗﻴﺎﻡ
ﻟﻴﻠﺘﻪ ﻭﺗﺨﺼﻴﺺ ﺫﻟﻚ ﺑﺪﻋﺔ , ﻭﻛﻞ ﺑﺪﻋﺔ ﺿﻼﻟﺔ "
ﺍﻧﺘﻬﻰ .
" ﻣﺠﻤﻮﻉ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ " ‏( 20/440 ‏)

An tambayi sheikh Muhammad Salihul Usaimeen
(RH)
dangane da azumi ranar 27 ga watan
rajab da
kuma tsayuwar dararen sa.
Sai ya amsa da cewa:
“Yin azumi ranar 27 ga watan Rajab
da tsayuwar
darensa kebance shi da haka bidi’a
ne, dukkan
bidi’a kuma batace”
Duba Majmu’u fatawa na Usaimeen
(20/440).

   Haka zalika Sayyidina umar R.A ya kasance yana bulala akan wadanda ke kamewa akan azumin Rajab, yana ce musu kuci abinci, wannan watane da ya kasance ake girmamawa a lokacin jahiliyya. [Ibn Abi shaibah ya fitar 3/102] da ibn kathir a cikin musnadil- faruk 1/285]

Haka zalika ibn umar R.A ya kasance idan yaga mutane suna wuce gona da iri akan Rajab, yana kyamar hakan!
[Sahih: ibn abi shaibah ya fitar 3/102]

Ibn Abbas ya kasance yana hani akan azumin Rajab gaba dayansa, saboda kada a maida shi ya zama abunda za'a rinka yi duk shekara, wato a maidashi ya zama idi.
[Sahih; Abdulrazak ya fitar 7854].

✏✏✏✏✏✏✏✏
HADISAN DA SUKA INGANTA AKAN WATAN RAJAB!
✏✏✏✏✏✏✏✏
=  "kuyi axumi a cikinshi kuma kuci abinci a cikinshi.
[Sahih irwa'ul galeel 958]

= Sha'aban yana tsakanin Rajab da Ramadhan, ana shagaltar da mutane akanshi(domin samun saukin Ramadan) a cikin sha'aban ake daukar ayukkan bayi, ina kwadayin/inason kada a daga ayyukana face ina azumi.
[Isnadinsa mai kyau ne, silsilatus-sahiha 1898]

✏✏✏✏✏✏✏✏
HADISSAI DA'IFAI WADANDA MASU AZUMIN RAJAB KE KAFA HUJJA DASU.!!!
✏✏✏✏✏✏✏✏

= A cikin Aljanna akwai wani gulbi, ana kiransa Rajab, ruwansa suna da fari wanda farin yafi na nono, duk wanda yayi azumin Rajab na rana daya, Allah zai shayar dashi daga wannan gulbin.[Silsilatu-dha'ifah 1898]

= Rajab watan Allah, Sha'aban wata na(manzon Allah), Ramadan watan Al'umma ta.
Da'ifi ne, silsilatu-dha'ifah 4400]

= Darare guda biyar ba'a maida Addu'ah: 1. Farkon Daren Rajab. 2. Daren Rabin watan sha'aban. 3. Daren jumu'ah.  4. Daren karamar sallah. 5. Daren babbar sallah.
[Maudu'i ne, silsilatu-dha'ifah 1452]

= Rajab watane mai girma, Allah na lunka lada idan kayi aikin Alkhairi a cikinsa, duk wanda yayi azumin Rajab na kwana daya,kamar yayi azumin shekara. Duk wanda yayi na kwana bakwai, za'a rufe mashi kofofin wutar jahannama bakwai. wanda yayi na kwana takwas, za'a bude mashi kofofin Aljanna takwas. Wanda yayi na kwana sha biyar, mai kira zaiyi kira a sama yace; an gafarta maka abunda ya gabata na laifuka...[maudu'i ne, silsilatu-dha'ifah 5413]

✏✏✏✏✏✏✏✏
RUBABBUN HADISSAN DA YAN SHI'AH KE KAFA HUJJA DASU AKAN FALALAR WATAN RAJAB.
✏✏✏✏✏✏✏✏
Daga Baban hassan (A.S) yace; Annabi Nuhu (A.S) ya tuka jirgin ruwa a farkon watan Rajab, sai ya umurci wadanda ke tare dashi da su azumci wannan ranar, yace; "duk wanda ya azumci wannan ranar Allah zai nisanta shi da wuta na tsawon tafiyar shekara daya.

=Daga Abi Ja'afar, Muhammad ibn Aliyu(A.S) yace; duk wanda yayi azumi a Rajab na rana daya, a farkon Rajab ko tsakiyarsa ko karshensa, Allah ya wajabta mashi shiga Aljanna, kuma Allah zai sanya shi a tare damu a cikin darajojinmu na Ahlul baiti a ranar kiyama, wanda yayi na kwana biyu, Allah zai gafarta mashi duk zunubbanshi da suka gabata, wanda yayi na kwana uku, Allah zai gafarta mashi abunda ya gabatar na zunubi da wanda zaiyi a gaba sannan za'a bashi damar ceton yan uwanshi ma'abota zunubi...

= As-sadik Ja'afar  ibn Muhammad yace; "kada ka bari ranar ashirin da bakwai ga Rajab ta wuce ba tare da ka azumceta ba! Domin a ranar ne aka saukar wa Annabi Muhammad s.a.w Annabta...

Duka wadannan zaka samesu a cikin littafi mai suna FALALAR WATANNI UKU, wanda gingimemen malamin Shi'ah mai suna MUHAMMAD IBN ALIYU IBN HUSSAIN IBN MUSA AL-QUMMY ya rubuta.
Allah ka la'anci qummy.

  A takaice wadannan sune hujjoji na dangane da rashin ingancin azumin Rajab(azumin tsofaffi), duk wanda yake ganin akwai Gyara matukar gyaran nashi ya inganta hadisi ne ko aya ina maraba dashi kwarai da gaske.

Allah ya hadamu dani daku da sauran musulmai a cikin Aljannah.

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH...```


Copyright©
Dalibinku
*_Hashim Suraj Uba Tsamiya {ABU SINÃN}_*
☎08064734911
📞09030201868

http://abbansinan.WordPress.com

http://hashimtsamiya.blogspot.com

http://abusinan.blogspot.com

atstsamawy@gmail.com

17-07-1438AH
15-04-2017AC

Wednesday, 5 April 2017

لا إله إلا الله

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*BAYANIN MA'ANAR LAA'ILAHA IL-LALLAHU!!!*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*_001_*

_Rubutawa:_ *Hashim Suraj Uba Tsamiya(ABU SINÃN)*

*بسم الله الرحمن الر حيم*

*الحمد لله رب العالمين، وصلى الله وسلم وبارك على نبينا محمد وعلى آله وصحبه أجمعين.*

```Da farko ya kamata musan cewa ita wannan Kalmar itace ke rabewa tsakanin musulmi da wanda ba musulmi ba!
Wannan Kalmar akan ta aka aiko dukkan Annabawa!
Itace Kalmar dake tabbatar da tsoron Allah na hakika!
Itace igiyar nan mai karfi, wacce duk Wanda ya riketa zata kaishi Aljanna!

Abin lura: Wannan Kalmar ba fadarta a baki ko da halshe tare da jahiltar ma'anarta ke sanya musuluncinka ya inganta ba!

Domin kuwa munafukai suna fadarta a bakunansu, amma kuma Allah yace" suna chan kasan wuta" a suratun nisa'i aya ta 145, tare da cewa suna Sallah suna sadaka, watakila har wurin wa'azi suna halarta.

Abunda ya kamata ga duk wanda ya fadeta, toh ya san ma'anarta har a zuciya ya kudurceta(ma'anarta, sharuddanta, falalarta, da abunda ta kunsa na tauhidi da akeeda) dole ne kaso Kalmar, kaso mai son Kalmar, dole ne ka yaki duk mai adawa da Kalmar ko mai saba mata.

Ita Kalmar LAA'ILAHA- IL-LALLAH! korewa ne da kuma tabbatarwa. Kore ilahantaka ga duk wani wanda ba Allah ba! Koda kuwa Manzo ne, ko Annabi, ko Mala'ika, ko wani mutumin kirki, ko gausi ko waliyyi koma Waye!  Tare da tabbatar da ilahantaka ga Allah shi kadai.

Na daga cikin mas'alolin jahiliyya wanda Annabi Muhammad s.a.w ya saba musu; Bautar mutanen kwarai ta Hanyar Neman biyan bukatunsu da nufin su nema musu ceto a wurin Allah, saboda zatonsu akan cewa Allah na son hakan. Kamar yadda Allah s.w.t yake cewa;
*ويعبدون من دون الله ما لا يضرهم ولا ينفعهم ويقولون هؤلاء شفعؤنا عند الله.* {يونس ١٨}

Ma'ana: "Suna bautar wani wanda ba Allah ba, Wanda bai iya cutar dasu, kuma bai iya amfanar dasu, har ma zakuji suna fada cewa wadancan sune masu cetonmu a wurin Allah"

Wannan ayar in muka lura zatayi aiki ga masu Dariku da yan shi'ah! Saboda suma zakuji suna fadar irin wadannan kalmomin, bari ma, wani lokaci nasu sunfi muni da hadari.

Muna rokon Allah s.w.t ya tabbatar damu akan tauhidi da akeeda Allah ka kara mana Ikhlasi.

Wannan mukaddima ce, amma bayanin zaizo a fitowa ta gaba insha Allahu.

Copyright©
Hashim Suraj Uba Tsamiya(ABU SINÃN)
08064734911```

http://abbansinan.WordPress.com

http://hashimtsamiya.blogspot.com

http://abusinan.blogspot.com

atstsamawy@gmail.com

Thursday, 30 March 2017

QARYA ADO A WURIN YAN SHI'AH

*'KARYA ADDININ YAN SHI'AH!!!*
**

**

**
```Don haka ne ibn Taimiyya a cikin minhajis-sunnah 1/59 yake cewa; Malamai ma'abota ilimi sunyi ittafaki(sun hadu) akan hakaitowa da ruwayoyi da isnadi akan cewa yan Shi'ah(Rafidhawa) makaryata ne na gaske, kuma karya a wajensu dadadden abune ba wai yau suka fara ba.
Haka shima ABU HATIM-ARRAZY yake cewa naji yunus ibn Abdul-a'ala yana cewa; Ash-hab ibn Abdul-aziz  yace: An tambayi IMAMU MALIK akan yan shi'ah? Sai IMAMU MALIK yace; kada kuyi magana dasu! Kada Ku  ruwaito magana ko wani Abu da zai amfani Al'umma daga garesu! Domin su makaryata ne.

Wannan kuwa kowa na iya gasgata hakan a wannan zamani da muke ciki

((YAA KU WADANDA SUKAYI IMANI, KU KARE KAWUNANKU DA IYALANKU DAGA WUTA! WACCE MAKAMASHINTA MUTANE DA DUWATSU))

Allah ka  kare musulmai daga makirci da sharrin yan Shi'ah a duk inda suke```

Copyright©
*Hashim Surajo Uba Tsamiya (ABU SINÃN)*
📞08064734911☎

http://abbansinan.WordPress.com

http://hashimtsamiya.blogspot.com

http://abusinan.blogspot.com

atstsamawy@gmail.com

Monday, 13 March 2017

HADISAN QARYA

HADISAN KARYA DA YAUDARAR JAMA'A
❇ ﻣﻦ ﻛﺬﺏ ﻋﻠﻲ ﻣﺘﻌﻤﺪ ﻓﻠﻴﺘﺒﻮﻉ ﻣﻘﻌﺪﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺎﺭ ❇
________________________________________
SHEIKUL ISLAM' IBNI TAIMIYYA'' BABBAN MUJAHIDIN MUSULUNCHI' YA TATARO WASU RUBABBUN HADISAI DA YA'N BIDI'A DA RAFITHAWA' SUKA DADE SUNA YAWO DASU SUNA YAUDARAR JAMA'A SUNA MAIDASU YA'N BIDI'A, KO KUMA SU HANA WASU YA'N BIDI'A DIN FAHIMTAR SUNNAR ANNABI SAWW "
IBNI TAIMIYYA'' YA WALLAFA LITTAFI
GUDA NA IRIN WADAN CHAN MUGGAN HADISAN, KAMAR SU!!!
1 WAI WANI MAWAKI' DA AKE KIRA ABU MAHZURA" YA TABA ZUWA GUN ANNABI SAWW " YA RERAWA ANNABI'' KASIDA' ACHIKI HAR YANA CEWA,
* ﻗﺪﻟﺴﻌﺖ ﺣﻴﺔ ﺍﻟﻬﻮﻯ ﻛﺒﺪﻱ . ّ. . ﻓﻼ ﻃﺒﻴﺐ ﻭﻻ ﺭﺍﻗﻰ * ﺇﻟﻰ ﺁﺧﺮﻫﺎ .
WAI SABODA JIN DADI HAR ANNABI SAWW'' YA CIRE MAYAFINSA YABAWA MAWAKIN KYAUTA,
IBNI TAIMIYYA'' YACE DUK MALAMAN HADISI' SUNCE, WAN NAN KARYA AKAYIWA ANNABI SAWW "
HAKAMA IBNI QAYYIM" A [MAS'ALATIS SAMA'A] DA ALIYUL QARY"' A [ AL'ASRARUL MARFU'A] DUK SUNCE WAN NAN HADISI' BASHIDA ASALI, KARYA CE KAWAI, HAKA BAI FARU BA,
2 WAI ANNABI SAWW " YACEWA SAYIDNA ALIYU''
* ﻳﺎ ﻋﻠﻲ ' ﺇﺗﺨﺬ ﻟﻚ ﻧﻌﻠﻴﻦ ﻣﻦ ﺣﺪﻳﺪ، ﻭﺃﻓﻨﻬﻤﺎ ﻓﻰ ﻃﻠﺐ ﺍﻟﻌﻠﻢ *
YA KAI ALIYU" KA KERA TAKALMIN KARFE' KAYITA TAFIYA NEMAN ILIMI' DASHI HAR SAI TAKALMIN YA MUTU,
IBNI TAIMIYYA'' CHIKIN [MAJMU'UL FATAWA] YACE,
WAN NAN BA ZANCEN ANNABI'' BANE,
HAKA MA ALIYUL QARY'' ACHIKIN [ KASHFUL HUFA'A] YACE WAN NAN HADISI' KIRKIRO SHI AKAYI,
3 WAI ANNABI SAWW'' YANA CEWA SAYIDNA ALIYU''
* ﺍﻧﺎ ﻣﺪﻳﻨﺔ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻭﻋﻠﻲ ' ﺑﺎﺑﻬﺎ، ﻓﻤﻦ ﺍﺭﺍﺩ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻓﻠﻴﺄﺗﻪ ﻣﻦ ﺑﺎﺑﻪ *
NI NE BIRNIN ILIMI' KAI KUMA ALIYU'' KAINE KOFAR BIRNIN, DAN HAKA DUK MAI NEMAN ILIMI' TO YABIYO TA KOFAR'
WAN NAN HADISI' RUWAYAR SA TAKAI GOMA, GALIBI
KUMA ANA JINGINAWA ABDULLAHI DAN ABBAS'' RUWAYOYIN,
AL'BANY'' A [TAKHRIJIL MISHKAT] DA IBNI JAUZY" A
[ AL'KAMIL FI THUA'FA'A] DA [AL'BIDAYA WANNIHAYA] DA [ TAZKIRATUL HUFFAZ] DUK SUN TABBATAR DA CEWA WAN NAN HADISI' KARYACE TSAGWARO' BA INDA ANNABI'' YA FADA,
4 WAI AN TARI' ANNABI SAWW " DA KIDAN BANDIRI' LOKACHIN DA YA ISO MADINA' YAYIN HIJIRA' ANA RERA KASIDA' ANA CEWA,
* ﻃﻠﻊ ﺍﻟﺒﺪﺭ ﻋﻠﻴﻨﺎ .... ﻣﻦ ﺛﻨﻴﺎﺕ ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ، ﺇﻟﻰ ﺁﺧﺮﻫﺎ ،
WAI YA'N MATA' SUNYITA RERAWA ANNABI'' WAN NAN WAKAR' HAR SHI KUMA YAKE CE MUSU,
* ﻫﺰﻭﺍ ﻛﺮﺍﺑﻴﻜﻢ ﺑﺎﺭﻙ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻴﻜﻢ *
WAI HAR KYAUTA YAYI MUSU YANA SA MUSU AL'BARKA,
AL'IRAQY'' ACHIKIN [ SHARHIN TASRYB] DA [TAKHRIJ NA AL'IHYA] DA [FATHUL BARY]
DUK AN TABBATAR DA KARYAR WAN NAN RUWAYAR SAMSAM BATA INGANTA BA, KADA WANI DAN BANDIRI' YA YAUDARE KA, DAN UWA,
5 WAI AN TAMBAYI ANNABI SAWW'' CEWA , TUN YAUSHE ALLAH YABAKA ANNABTA?? SAI YACE,
* ﻛﻨﺖ ﻧﺒﻴﺎ ﻭﺁﺩﻡ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻤﺎﺀ ﻭﺍﻟﻄﻴﻦ، ﻭﻛﻨﺖ ﻧﺒﻴﺎ ﻭﻻ ﺁﺩﻡ ﻭﻻ ﻣﺎﺀ ﻭﻻ ﻃﻴﻦ ،
AI AMBANI ANNABTA' TUN A'DAMU'' YANA TSAKANIN RUWA DA TABO' KAI BAMA HAKA BA,
AMBANI ANNATA' TUN BABU A'DAMU' BABU RUWA BABU TABO'
IBNI TAIMIYYA''
YACE WAN NAN MAGANAR BANZA CE,
BA GASKIYA BANE,
6 WAI ANNABI'' YACE ,
* ﻣﻦ ﻭﺳﻊ ﻋﻠﻰ ﺍﻫﻠﻪ ﻓﻰ ﻳﻮﻡ ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ ﻭﺳﻊ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﺳﺎﺋﺮ ﺳﻨﺘﻪ،
DUK WANDA YA YALWATA GIDANSA DA ABINCHI A RANAR A'SHURA' TO ALLAH " ZAI YALWATA MASA A SAURAN SHEKARU' NA GABA,
WANI DALIBIN IMAM AHMAD''
YACE NA TAMBAYI AHMAD" MATSAYIN WAN NAN HADISIN,
SAI YACE MIN AI WAN NAN HADISIN BASHIDA ASALI, WATO MAGANA CE KAWAI TA BANZA, TA KAN TITI ,
7 WAI WARAN ANNABI SAWW'' YANA ZAUNE A MASALLACHI YA MIKE KAFA, SAI KUWA ALLAH SWT'' YAYI MASA WAHAYI YANA CE DASHI
* ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻣﺎ ﺃﻧﺖ ﻓﻰ ﻣﻨﺰﻝ ﻋﺎﺋﺸﺔ "
YA MUHAMMAD'' BAFA ADAKIN A'ISHA' KAKE BA, DAN HAKA NADE KAFARKA,
WAN NAN MA MAGANAR BANZA CE,
HAR BARCHI SAHABBAI'' SUNAYI A MASALLACHI,
8 WAI ALLAH SWT'' YANA CEWA,
* ﻣﺎ ﻭﺳﻌﻨﻰ ﺳﻤﺎﺋﻲ ﻭﺍﻷﺭﺿﻲ ، ﺑﻞ ﻭﺳﻌﻨﻲ ﻗﻠﺐ ﻋﺒﺪﻱ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ *
WAI SAMA' DA KASA' DUK BASU ISHENI BA, MA'ANA SUNYI MIN MATSI' AMMA ZUCIYAR BAWANA MUMINI' TA WADACE NI,
IBNI TAIMIYYA'' YACE
WAN NAN ISRA'ILIYYAT" NE
BABU WANI CHIKAKKEN ISNADI' GA WAN NAN MAGANAR
DOMIN DUK WANDA YA QUDURE CEWA ZATIN ALLAH'' YANA SAUKA AKAN ZUCIYAR DAN ADAM' TO WAN NAN YAFI NASARA' KAFIRCHI,
9 WAI ANNABI'' CEWA ,
* ﺣﺐ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺭﺍﺱ ﻛﻞ ﺧﻄﻴﺌﺔ *
WAI ANNABI'' YACE, SAN DUNIYA' SHINE TUSHEN DUK WATA BARNA TA KUSKURE, KOMA TA GANGANCHI,
ANA JINGINAN
WAN NAN RUWAYAR GA
JUNDUBI BIN ABDULLAHI AL'BAJLY"
AMMA BATADA WANI ISNADI' ZUWA GA ANNABI SAWW''
DAN HAKA BA HADISI' BANE ,
10 WAI ANNABI " YACE,
* ﺍﻟﺸﻴﺦ ﻓﻲ ﻗﻮﻣﻪ ﻛﺎﻟﻨﺒﻲ ﻓﻰ ﺍﻣﺘﻪ ،
TSOHO ACHIKIN DANGINSA KAMAR ANNABI NE ACHIKIN AL'UMMAR SA,
IBNI TAIMIYYA''
YACE WAN NAN BA MAGANAR ANNABI SAWW " BACE,
WANI DAN BARIKI NE KAWAI YA
SHARARA TA,
---------------------
GODIYA TA MUSAMMAN GA
MALAMAN MU NA SUNNAH'' DA SUKA TSAYA SOSAI WAJAN HASKAWA AL'UMMA FITILAR SHIRIYA' DAN SAMUN RABON LAHIRA, ALLAH SWT'' YA TABBATAR DA MU AKAN SUNNAR
MANZON SA SAWW''

HADISAN QARYA

HADISAN KARYA DA YAUDARAR JAMA'A
❇ ﻣﻦ ﻛﺬﺏ ﻋﻠﻲ ﻣﺘﻌﻤﺪ ﻓﻠﻴﺘﺒﻮﻉ ﻣﻘﻌﺪﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺎﺭ ❇
________________________________________
SHEIKUL ISLAM' IBNI TAIMIYYA'' BABBAN MUJAHIDIN MUSULUNCHI' YA TATARO WASU RUBABBUN HADISAI DA YA'N BIDI'A DA RAFITHAWA' SUKA DADE SUNA YAWO DASU SUNA YAUDARAR JAMA'A SUNA MAIDASU YA'N BIDI'A, KO KUMA SU HANA WASU YA'N BIDI'A DIN FAHIMTAR SUNNAR ANNABI SAWW "
IBNI TAIMIYYA'' YA WALLAFA LITTAFI
GUDA NA IRIN WADAN CHAN MUGGAN HADISAN, KAMAR SU!!!
1 WAI WANI MAWAKI' DA AKE KIRA ABU MAHZURA" YA TABA ZUWA GUN ANNABI SAWW " YA RERAWA ANNABI'' KASIDA' ACHIKI HAR YANA CEWA,
* ﻗﺪﻟﺴﻌﺖ ﺣﻴﺔ ﺍﻟﻬﻮﻯ ﻛﺒﺪﻱ . ّ. . ﻓﻼ ﻃﺒﻴﺐ ﻭﻻ ﺭﺍﻗﻰ * ﺇﻟﻰ ﺁﺧﺮﻫﺎ .
WAI SABODA JIN DADI HAR ANNABI SAWW'' YA CIRE MAYAFINSA YABAWA MAWAKIN KYAUTA,
IBNI TAIMIYYA'' YACE DUK MALAMAN HADISI' SUNCE, WAN NAN KARYA AKAYIWA ANNABI SAWW "
HAKAMA IBNI QAYYIM" A [MAS'ALATIS SAMA'A] DA ALIYUL QARY"' A [ AL'ASRARUL MARFU'A] DUK SUNCE WAN NAN HADISI' BASHIDA ASALI, KARYA CE KAWAI, HAKA BAI FARU BA,
2 WAI ANNABI SAWW " YACEWA SAYIDNA ALIYU''
* ﻳﺎ ﻋﻠﻲ ' ﺇﺗﺨﺬ ﻟﻚ ﻧﻌﻠﻴﻦ ﻣﻦ ﺣﺪﻳﺪ، ﻭﺃﻓﻨﻬﻤﺎ ﻓﻰ ﻃﻠﺐ ﺍﻟﻌﻠﻢ *
YA KAI ALIYU" KA KERA TAKALMIN KARFE' KAYITA TAFIYA NEMAN ILIMI' DASHI HAR SAI TAKALMIN YA MUTU,
IBNI TAIMIYYA'' CHIKIN [MAJMU'UL FATAWA] YACE,
WAN NAN BA ZANCEN ANNABI'' BANE,
HAKA MA ALIYUL QARY'' ACHIKIN [ KASHFUL HUFA'A] YACE WAN NAN HADISI' KIRKIRO SHI AKAYI,
3 WAI ANNABI SAWW'' YANA CEWA SAYIDNA ALIYU''
* ﺍﻧﺎ ﻣﺪﻳﻨﺔ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻭﻋﻠﻲ ' ﺑﺎﺑﻬﺎ، ﻓﻤﻦ ﺍﺭﺍﺩ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻓﻠﻴﺄﺗﻪ ﻣﻦ ﺑﺎﺑﻪ *
NI NE BIRNIN ILIMI' KAI KUMA ALIYU'' KAINE KOFAR BIRNIN, DAN HAKA DUK MAI NEMAN ILIMI' TO YABIYO TA KOFAR'
WAN NAN HADISI' RUWAYAR SA TAKAI GOMA, GALIBI
KUMA ANA JINGINAWA ABDULLAHI DAN ABBAS'' RUWAYOYIN,
AL'BANY'' A [TAKHRIJIL MISHKAT] DA IBNI JAUZY" A
[ AL'KAMIL FI THUA'FA'A] DA [AL'BIDAYA WANNIHAYA] DA [ TAZKIRATUL HUFFAZ] DUK SUN TABBATAR DA CEWA WAN NAN HADISI' KARYACE TSAGWARO' BA INDA ANNABI'' YA FADA,
4 WAI AN TARI' ANNABI SAWW " DA KIDAN BANDIRI' LOKACHIN DA YA ISO MADINA' YAYIN HIJIRA' ANA RERA KASIDA' ANA CEWA,
* ﻃﻠﻊ ﺍﻟﺒﺪﺭ ﻋﻠﻴﻨﺎ .... ﻣﻦ ﺛﻨﻴﺎﺕ ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ، ﺇﻟﻰ ﺁﺧﺮﻫﺎ ،
WAI YA'N MATA' SUNYITA RERAWA ANNABI'' WAN NAN WAKAR' HAR SHI KUMA YAKE CE MUSU,
* ﻫﺰﻭﺍ ﻛﺮﺍﺑﻴﻜﻢ ﺑﺎﺭﻙ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻴﻜﻢ *
WAI HAR KYAUTA YAYI MUSU YANA SA MUSU AL'BARKA,
AL'IRAQY'' ACHIKIN [ SHARHIN TASRYB] DA [TAKHRIJ NA AL'IHYA] DA [FATHUL BARY]
DUK AN TABBATAR DA KARYAR WAN NAN RUWAYAR SAMSAM BATA INGANTA BA, KADA WANI DAN BANDIRI' YA YAUDARE KA, DAN UWA,
5 WAI AN TAMBAYI ANNABI SAWW'' CEWA , TUN YAUSHE ALLAH YABAKA ANNABTA?? SAI YACE,
* ﻛﻨﺖ ﻧﺒﻴﺎ ﻭﺁﺩﻡ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻤﺎﺀ ﻭﺍﻟﻄﻴﻦ، ﻭﻛﻨﺖ ﻧﺒﻴﺎ ﻭﻻ ﺁﺩﻡ ﻭﻻ ﻣﺎﺀ ﻭﻻ ﻃﻴﻦ ،
AI AMBANI ANNABTA' TUN A'DAMU'' YANA TSAKANIN RUWA DA TABO' KAI BAMA HAKA BA,
AMBANI ANNATA' TUN BABU A'DAMU' BABU RUWA BABU TABO'
IBNI TAIMIYYA''
YACE WAN NAN MAGANAR BANZA CE,
BA GASKIYA BANE,
6 WAI ANNABI'' YACE ,
* ﻣﻦ ﻭﺳﻊ ﻋﻠﻰ ﺍﻫﻠﻪ ﻓﻰ ﻳﻮﻡ ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ ﻭﺳﻊ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﺳﺎﺋﺮ ﺳﻨﺘﻪ،
DUK WANDA YA YALWATA GIDANSA DA ABINCHI A RANAR A'SHURA' TO ALLAH " ZAI YALWATA MASA A SAURAN SHEKARU' NA GABA,
WANI DALIBIN IMAM AHMAD''
YACE NA TAMBAYI AHMAD" MATSAYIN WAN NAN HADISIN,
SAI YACE MIN AI WAN NAN HADISIN BASHIDA ASALI, WATO MAGANA CE KAWAI TA BANZA, TA KAN TITI ,
7 WAI WARAN ANNABI SAWW'' YANA ZAUNE A MASALLACHI YA MIKE KAFA, SAI KUWA ALLAH SWT'' YAYI MASA WAHAYI YANA CE DASHI
* ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻣﺎ ﺃﻧﺖ ﻓﻰ ﻣﻨﺰﻝ ﻋﺎﺋﺸﺔ "
YA MUHAMMAD'' BAFA ADAKIN A'ISHA' KAKE BA, DAN HAKA NADE KAFARKA,
WAN NAN MA MAGANAR BANZA CE,
HAR BARCHI SAHABBAI'' SUNAYI A MASALLACHI,
8 WAI ALLAH SWT'' YANA CEWA,
* ﻣﺎ ﻭﺳﻌﻨﻰ ﺳﻤﺎﺋﻲ ﻭﺍﻷﺭﺿﻲ ، ﺑﻞ ﻭﺳﻌﻨﻲ ﻗﻠﺐ ﻋﺒﺪﻱ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ *
WAI SAMA' DA KASA' DUK BASU ISHENI BA, MA'ANA SUNYI MIN MATSI' AMMA ZUCIYAR BAWANA MUMINI' TA WADACE NI,
IBNI TAIMIYYA'' YACE
WAN NAN ISRA'ILIYYAT" NE
BABU WANI CHIKAKKEN ISNADI' GA WAN NAN MAGANAR
DOMIN DUK WANDA YA QUDURE CEWA ZATIN ALLAH'' YANA SAUKA AKAN ZUCIYAR DAN ADAM' TO WAN NAN YAFI NASARA' KAFIRCHI,
9 WAI ANNABI'' CEWA ,
* ﺣﺐ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺭﺍﺱ ﻛﻞ ﺧﻄﻴﺌﺔ *
WAI ANNABI'' YACE, SAN DUNIYA' SHINE TUSHEN DUK WATA BARNA TA KUSKURE, KOMA TA GANGANCHI,
ANA JINGINAN
WAN NAN RUWAYAR GA
JUNDUBI BIN ABDULLAHI AL'BAJLY"
AMMA BATADA WANI ISNADI' ZUWA GA ANNABI SAWW''
DAN HAKA BA HADISI' BANE ,
10 WAI ANNABI " YACE,
* ﺍﻟﺸﻴﺦ ﻓﻲ ﻗﻮﻣﻪ ﻛﺎﻟﻨﺒﻲ ﻓﻰ ﺍﻣﺘﻪ ،
TSOHO ACHIKIN DANGINSA KAMAR ANNABI NE ACHIKIN AL'UMMAR SA,
IBNI TAIMIYYA''
YACE WAN NAN BA MAGANAR ANNABI SAWW " BACE,
WANI DAN BARIKI NE KAWAI YA
SHARARA TA,
---------------------
GODIYA TA MUSAMMAN GA
MALAMAN MU NA SUNNAH'' DA SUKA TSAYA SOSAI WAJAN HASKAWA AL'UMMA FITILAR SHIRIYA' DAN SAMUN RABON LAHIRA, ALLAH SWT'' YA TABBATAR DA MU AKAN SUNNAR
MANZON SA SAWW''

RAMADAN TAFSEER

MASALLACN ABU HURAIRA YAR'YARA TSAFE

Complete Ramadan tafseer 2016 daga masallacin Abi hurairah yar yara tsafe, Wanda limamin (masallaccin jumu'ah Na Abu Huraira area 2. Tsafe) yake gabarwa, wato *Malam Sani Liman?? tsafe(Abu hurairah)*
Shiga links dake kasa domin saukewa cikin sauki
� � � � � � � �
01 http://darulfikr.com/s/7577
02
http://darulfikr.com/s/7578
03
http://darulfikr.com/s/7579
04
http://darulfikr.com/s/7580
05
http://darulfikr.com/s/7581
06
http://darulfikr.com/s/7582
07
http://darulfikr.com/s/7583
08
http://darulfikr.com/s/7584
09
http://darulfikr.com/s/7585
010
http://darulfikr.com/s/7586
011
http://darulfikr.com/s/7587
012
http://darulfikr.com/s/7588
013
http://darulfikr.com/s/7589
014
http://darulfikr.com/s/7590
015
http://darulfikr.com/s/7591
016
http://darulfikr.com/s/7592
019
http://darulfikr.com/s/7593
020
http://darulfikr.com/s/7594
021
http://darulfikr.com/s/7595
022
http://darulfikr.com/s/7596
023
http://darulfikr.com/s/7597
024
http://darulfikr.com/s/7598
025
http://darulfikr.com/s/7599Ramadan
026
http://darulfikr.com/s/7600
027
http://darulfikr.com/s/7601
028
http://darulfikr.com/s/7602
029
http://darulfikr.com/s/7603
030
http://darulfikr.com/s/7604
Http://abuhurairah.mywapblog.com
Darulfikr.com takuce domin yada Sunnah

BULUGUL MARAM

BULUGUL MARAM❗
KAMAR KOWACE ASABAR YAUMA MUNDORA INDA MUKA KWANA ACIKIN KARATUN LITTAFIN BULUGUL MARAM,  DAGA MASALLACIN ABI HURAIRAH 'YARYARA TSAFE,  DAGA BAKIN LIMAN SANI LIMAN TSAFE.
HARYAU MUNA CIKIN BABUS SUFFATUS SALAT,  MAL YA BUDEDA HADITHIN ABDULLAHI DAN UMAR INDA YAKE CEWA: MANZON ALLAH (S. A. W),  YA KASANCE YANA DAGA HANNUWANSA DAURA DA KAFADARSA YAYINDA ZAIYYI KABBARA. HADITHIN KUMA (MUTTAFAQUN ALAIHI). WATA RUWAYA KUMA TACE YANA DAGASU DAURA DA KUNNUWANSA,  DADAI SAURAN HADITHAI DA MAL YA KORO ACIKIN BABIN,  DONJIN CIKAKKEN KARATUN ATARBI AUDIO DA ZAMU TURO YANZU INSHA ALLAHU.
MUNA ROQON ALLAH YA SAKAWA MAL DA ALKHAIRI AMIN THUMMA AMIN.

MUHADARA A GARIN YANDOTON DAJI

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌
MASALLACIN ABU HURAIRA YAR'YARA TSAFE

MUHADARA DA MALAM YAYI A' GARIN YANDOTO DAJI.

ALLAH BASHI AMSA AIKI MATUKA AIKIN BABU TAUHIDI.

👉ALLAH (S. W. T) YANA CEWA ZAMU GABATAR DA AYYUKAN DA AL'UMMAH SUKAYI WADANDA BABU TAUHIDI,  SAI MU SANYA AIKIN YA ZAMA WATA KURA WA TSAR--TSA. HAKA ALLAH ZAIYI MA AIKIN DA  BABU TAUHIDI A' CIKI

MALAM YAYI TAMBAYA CEWA MEYE AKIDA?

             AKIDAH A' MUSULUNCI ITA CE:--
             ----------------------------------------------------

AKIDA (TAUHIDI)  SHI NE  KAYI IMANI DA ALLAH KAI TSAYE,  KAYI IMANI DA MALA'IKUN ALLAH,  KAYI IMANI DA LITTAFAN ALLAH,  KAYI IMANI DA MANZONNIN ALLAH,  KAYI IMANI DA RANAR TASHIN KIYAMA, KAYI IMANI DA KADDARA MAI KYAU CE KO MARA KYAU, KAYI IMANI GA DUKKAN ABUNDA YAZO CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA, SANNAN KAYI IMANI DA ABUN DA YAZO CIKIN KARANTARWA MANZON ALLAH, DA ABUNDA SALAF SUKA HADU AKAN SA NA AKIDA,  KANA KAYI DA'A GA MANZON ALLAH AKAN DUK ABUNDA YAZO MAKA DA SHI.

   HANYOYIN DA ZAMUBI DOMIN TABBATAR DA AKIDAH A' CIKIN ZUCIYARMU

1. YIMA ALLAH DA'A DA KWADAYIN SAMUN RAHAMAR SA,  MALAM YA KAWO HADISIN DA MANZON ALLAH (S. A. W) YACE MA SAHABBAI WANE AIKI KUKE MA ALLAH DOMIN KWADAYIN SHIGA ALJANNAH KOWA YAYI TA KAWO NASA, HAR DAI BILAL YA DAGA HANNU, SAI MANZON ALLAH YACE BANDA KAI BILAL MANZON ALLAH YACE NAJI TAKUN TAKALMAN A' CIKIN ALJANNAH SAI MANZON ALLAH YA TAMBAYI MALA'IKA CEWA TAFIYAR WA YAKEJI SAI YACE BILAL NE,  SAI MANZON ALLAH YA TAMBAYI BILAL AKAN AIKIN DA YA KEYI, SAI BILAL YACE KODA YAUSHE YANA ZAMA DA ALWALLAH,  IDAN KUMA TA KARE YANA YIN WATA, A' SANADIYAR HAKA ALLAH YA BA SHI ALJANNAH.

2. BARIN SABON ALLAH DON JIN TSORON AZABAR SHI

3. TUNTUNE A' CIKIN HALITTA SAMA,  DA KASA,

4. SANIN SUNAYEN ALLAH DA SIFFOFIN SA,  YA ZAMA WAJIBI KASAN SUNAYEN ALLAH,  DOMIN ALLAH YANA FUSHI DA WANDA BAI SAN SUNAYEN SHI BA.

5. YIN KOKARI
KA NEMI ILMI MAI AMFANI, MALAM YAYI BAYANI CEWA BA'A YIN SUNNAH BABU ILMIN SABODA HAKA WAJIBI NE KA NEMI ILMI.


6. ZAMA DA MUTANEN KIRKI NA KWARAI MASU  SON ADDININ, HAR MALAM YA KAWO HADISIN DA MANZON ALLAH YACE MUTUM YANA SAMAN ADDININ ABOKIN SA, KOWA YA NEMI MUTUMEN DA ZAIYI ABOTA DA SHI.


7. DAUWAMA AKAN AMBATON ALLAH A' KOWANE LOKACI


8. KOYI DA MANZON ALLAH A' CIKIN ABU BABBA, KO KARAMI, 



9. UMURNI DA AIKI NA KWARAI DA HANI DA MUGUN AIKI


10. YADDA DA ABUNDA ALLAH YA TSARA



11. GIRMAMA ALQURANI DA SUNNAH MANZON ALLAH

12. KOKARIN RIKO DA SUNNAH, IDAN KANA RIKO DA ITA SUNNAH BIDI'AH BATA SAMUN WURIN ZAMA

13. SHIGA CIKIN ADDINI BAKI DAYA



14.  HADAWA TSAKANIN NAFSO SHI.

KADAN KE NAN GAME DA ABUN DA MUNAZARA DA KUNSA,  WATO KASHI DAYA CIKIN GOMA NAYI BAYANI IDAN KA SAURARA ZAKA JI FIYE DA HAKA,

ALLAH YA BIYA MALAM AMIN.

BUGYATUL MISHTAQ

BUGYATUL MISHTAQ❗
Kamar kowace Lahadi yauma mun dora inda muka kwana acikin wannan littafi na BUGYATUL MISHTAQ.
IBN TAIMIYYAH yake cewa haqiqa ALLAH (S.W.A), Yana hadama bawa nau'i na ni'ima wanda ya wajaba ya gode masa, ko kuma jarabawa wadda ya wajaba yayi haquri akanta, kamar yanda abun ya kasance ranar 27 ga watan Ramadhan ranarne akayi yaqin BADAR, Kuma irin ranarce aka kashe SAYYIDINA ALIYU, Hakanan kuma abunda yafi shahara cewa ranar litinin acikin watan RABI'U AUWAL ne aka haifi MANZON ALLAH (S.A.W), Kuma a irin lokacinne yayi HIJIRA, kuma a irin ranarne ya rasu. Don haka kenan bawa mumini za'a iya jarabtarsa da abubuwa masu kyau wadanda zasu faranta masa rai, da kuma musibobi wadanda zasu baqanta masa rai duk alokaci guda, domin Dan Adam ya kasance mai haquri kuma mai godiya, to ya kake ganin abun idanya kasance a lokutta biyu  lissafafi daga nau'i guda.
Aqarshe IBN TAIMIYYAH Yayi bayanin dalilin rubuta wannan littafi cewa wasu jama'ane suka isko IBN TAIMIYYAH  da wata takarda wadda 'yan shi'ar Iran suka rubuta masu, sai IBN TAIMIYYAH ya karanta wannan takardar aqarshe ya walwale masu matsalar kuma suka gamsu suka fahimta.
Wannan kadan kenan daga cikin abunda karatun yau ya qunsa, don jin cikakken karatun a tarbi audio da zamu turo bada dadewaba insha Allah.
Muna roqon Allah ya sakawa mal da alkhairi amin thumma amin.