HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA
DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE
A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #TSAFTA
Godiya ta tabbata madaukakin sarki, Muna gode masa muna neman taimakonsa, Muna neman yakare daga sharrin kawunan mu,
Na shaida babu abun bautawa da gaskiya sai ALLAH Baya da abokin taraiya, Na shaida Annabi Muhammadu bawan sa ne kuma manzonsa,
Tsira da amincin ALLAH Su kara tabbata ga manzo tsira da alayen da sahabban sa da dukan wadanda suka bayan su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako!
Yan uwa musulmi a yau khudbar zatayi magana ne akan Tsafta a addinin musulunci!
Addinin musulunci yayi umarni da tsafta a kowane bangare na rayuwa, Kama daga ta jiki da kaya da dukan dai wata mu'amula ta yau da kullun,
Tsafta tana daya daga cikin umarni na farko farko da aka fara bayarwa a lokacin da musulunci yake da dumi duminsa,
Kamar yadda ALLAH Yake fada cikin suratul Muddasir cewa ''YA KAI MAI LULLUBI (Annabi Muhammad SAW) KA TASHI KAYI GARGADI KA GIRMAMA UBANGIJINKA KA TSAFTACE TUFAFIN KA''
Kunga wannan ayar tana kwadaitar damu kan tsafta, Hakama ALLAH Madaukakin sarki na cewa ''YAKU WADANDA KUKAYI IMANI IDAN KUN TSAYU GA SALLAH KU WANKE FUSKOKINKU DA KAFAFUNKU''
Yaku yan uwa musulmi kusani itafa tsafta ita ke jagoranta har mutane su soka su dinga taraiya dakai,
Yaku yan uwa musulmi daga cikin manyan ni'imomin da ALLAH Yayi mana itace ni'imar ruwan sama, Su kuwa ruwan sama suna zuwa ne dan tsaftace kasa daga datti, Da kazanta da shirka wadda shaida L.A ya qawata ma mutane yi, Kamar yadda ALLAH Madaukakin sarki yake cewa ''MUNA SAUKAR DA RUWAN SAMA DAN TSAFTACE KASA DAGA DATTI''
Yaku yan uwa musulmi tsafta tana da wani bagire a musulunci, Manzo rahama SAW Yana fada cikin wani hadisi cewa ''MAI TSAFTA ALLAH ZAI TADASHI YANA HASKE A FUSKA'' Ma'ana mai alwalla ita kuwa alwallah tsafta ce, Hakama manzo rahama SAW Yana fada cewa ''RANAR KIYAMA AL'UMMATA ZASU ZO DA HASKE A FUSKOKIN SU DA KAFAFUN SU SABODA ALWALLAR DA SUKA AIKATA A DUNIYA''
Tsafta muhimmacinta nada matuqar yawa, shinasa sa aka alaqanta duk wata ibada da tsafta kamar su sallah, Dawafi Karatun Qur'ani da sauran ibadu,
Yana daga cikin tsafta yawaita wanka kamar su na jumu'a kamar yadda manzon rahama SAW Yake cewa ''NAYI UMARNI DA WANKAN JUMU'A''
Hakama a wata ruwayar na cewa ''WANKA JUMU'A WAJIBI NE''
Mafi yawan wasu mutane na ganin kamar tsafta batada wata alaqa da addinin musulunci, Sam ba haka bane addinin musulunci shine addinin daya fara jaddadda tsafta a duniya,
Rashin tsafta dabi'ar ce ta mushrikai, Wata rana salmanul farisi ya fito sai wani mushriki yayi mai wata magana ta izgili yana cewa ''Naga abokin (wato yana nufin annabin Muhammad SAW) ku yana umartar ku da tsafta har a makeyi''
Hakika musulunci ya sanya tsafta a ciki yanki na imani, Kamar yadda hadisin manzon Tsira yake cewa ''TSARKI SHARADI NE NA IMANI'' Kaga idan kana da kazanta to lallai imanin ka nada rauni matuka!
Saboda matsayin tsarki da tsafta yasa malaman fiqhu suke yawaita gabata da tsafta ko tsarki a farko farko,
ALLAH Madaukakin sarki ya yabi mata kan yadda suke tsafta kamar yadda yake fada a cikin suratul baqarah cewa ''LALLAI ALLAH YANA SON MASU TUBA DA MASU TSAFTA''
Ana bukatar duk bayan mata sunyi tsarki na kowane jini suyi tsarki dan tsafta su sanya turare,
Musulunci yana wajabta wasu fannona da suka zama wajibi a aikata su har guda goma sha daya (11)
1- Tsaftace baki, Ma'ana tsaftace baki ta hanyar wankewa da Brush da macling, Ko aswaki ko wani mai na goge baki, kamar yadda hadisi ya umarta cewa ''KUYI ASWAKI DAN YANA TSAFTACE BAKI DAGA KAZANTA''
2-Tsaftace suma ko gashin kai, Ma'ana tsaftace gashin kai, Ko rage sa, Ko kuma shace sa, Ko kuma askesa, Hadisi daga manzo tsira na cewa ''WANDA ALLAH YA AZURTA DA GASHI YARINGA KARRAMA GASHIN'' Ma'ana ka tsaftace shi ta dawanchan hanyoyi, Kada kabar gashin ka lalace yayi babu kyan gani ba tsafta.
3-Tsaftace gidaje da massalatai da kofar gidaje da wurare kasuwanci, Kada kubar wajen shara ta taru ko kuma yayi kasha-kasha, hadisi ya tabbata daga manzo tsira cewa ''KU TSAFTACE FARFAJIYAR KU KADA KUYI KOYI DA YAHUDAWA DAN SUNA TARA SHARA TSAKAR GIDA ''
4-SANYA TURARE Ma'ana yawan amfani da turare dan kauda wari da kazanta, Anan ma hadisi ya tabbata daga manzo tsira cewa ''LALLAI ALLAH MAI KYAU NE KUMA YANASO YAGA ANA TSAFTA''
5-Tsaftace Massallatai, Kada mubar massallatan mu babu kyau, Annabi ya gargademu da kada muje massallaci ba tsafta ''WANDA YACI ALBASA KO TAFARNUWA KADA YAZO MASSALLACI''
6- Mata masu jinin al'ada ya zama wajibi su kyautata tsafta, yana da kyau su warware kitson su, su wanke ko ina tare amfani da turare a gabansu dan inganta tsaftar su,
7-Tsaftace jiki, Mu kula da tsaftace jiki ganin yadda yanzu muke cikin lokachin zafi, Kamar yadda yagabata khudbar wancan makon
8-Kula da sunnoni goma, Manzo tsira SAW Yana cewa ''YANA CIKIN FIDDA WATO (Sunnar asali ta yan adam) sune kamar haka,
-Rage gashin baki, a kula ba askewa ake nufi ba baki daya,
-Mucika gemu, Kammala gemu ba tare aske shi ba,
-Aswaki, Yawaita aswaki yana daga cikin sunnonin asali,
-Kuskure baki, Yawaita kuskure baki idan kaji yadan yi maka nauyi,
-Rage akaifa, A yawaita rage akaifa saboda akaifa shine ne ke daukar datti ta boye a cikin hannu
-Wanke hannu, Yawaita wanke hannu, Dan gudun kada a kwaso wata cuta,
-Rage gashin hamata, Yana da kyau rage ya, Dan anan cuttutuka suke boyewa,
-Gusar da gashin mara, Hadisi yazo daga manzo tsira cewa ''KADA MUSULMI YA KUSKURA YA WUCE KWANA ARBA'IN BAI KAUDA WADANNAN KAZANTAR BA''
9-Tsaftace hanyoyin da muke bi, Mu tsaftace hanyoyin da muke bi yau da kullun, Hadisi yazo daga manzo tsira cewa ''IMANI GIDA SABA'IN NE BABBA DAGA CIKI ITACE KALMAR LA'ILAHA ILALLAH KARAMA DAGA CIKIN KUWA ITACE GUSAR DA DATTI HANYA''
Yana da kyau koda gwalab ko fitila ce a aje a hanya dan ganin haske a hanya
10-Tsaftace abinci da ruwan mu, Kiyaye ruwan sha dana koramu, Da kuma tsaftace abinci, Manzo tsira SAW Yace ''IDAN KUN SHIGA GIDA KU KULLE IDAN ZASU KWANTA KU RUFE RANDA KU KASHE WUTA KU RUFE ABINCI'' saboda shaidan baya iya buda randar da aka rufe ko abincin da aka rufe, Yana da kyau a kula, Idan ba'a rufewa shaidan zai iya zuwa ya tofa miyau (Yawu) a ciki , Wanda haka zai kai ga bular cuta mai wuyar magani!
-Tsaftace wuraren da ruwa ke zama, kamar su rijiyoyi, Da gulabe da dam dama, Yana kyau yan uwa musulmi mu kiyaye,'' Manzo SAW Ya hana fitsari a cikin ruwa da basu gudu '' ya hana hakan ne dan gudun kada wani ya dauki cuta daga wani ,
Musulunci yayi dukan wadannan bayanan ne dan kare lafiya dan Adam musulmai, Da kuma shari'a ta karemu daga daukar duk wasu cuttutuka,
Yaku yan uwa musulmi mu kula dan kaucewa fadawa cikin halaka Saboda ALLAH Madaukakin sarki na cewa ''KADA KU JEFA KAWUNAN KU CIKIN HALA''
Muna rokon ALLAH Yagafarta mana, Ya bamu lafiya da zama lafiya, Yayi mana saukin zafin sama da kasa dana aljihu, Ya Allah ina tawasulli da wannan khudbar ka biya mana bukatun mu, Ka gafartawa mamatan mu, Kayi jagoranci ga shuwagabanni ka dora su a turba ta dai dai.
ALHAMDULILLAH
©®IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA
24/Rajab/1438
21/04/2017.